Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan sabon mafi ƙarancin albashi

Kano ita ce jiha ta farko da ta kafa kwamiti game da sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan sabon mafi ƙarancin albashi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin bayar da shawara kan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, wanda shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.

Gwamnatin ta kafa kwamitin ne sa’o’i 48 bayan amincewar shugaban ƙasa kan mafi ƙarancin albashin.

Kano ita ce jiha ta farko a Najeriya da ta kafa irin wannan kwamiti.

A ranar Talata ne gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin a fadar gwamnatin jihar ta hannun mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ibrahim Garba Shuaibu, mai magana da yawun mataimakin gwamnan, ya bayyana cewa kwamitin zai tsara yadda za a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da kuma bayar da shawarwari ga gwamnatin jihar.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi zai ƙara bunƙasa ci gaba a Jihar Kano.

Ya buƙaci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa cikin makonni uku, inda ya bayyana cewa an zaɓi mambobin ne bisa la’akari da cancantar su kuma ana sa ran za su samar da sakamakon da ya dace.

Shugaban kwamitin, Alhaji Usman Bala Muhammad, wanda shi ne mashawarci na musamman ga gwamnan kan harkokin jihar, ya yi godiya ga amanar da gwamnatin ta damƙa musu.

Ya ce aikin kwamitin zai yi tasiri sosai ga ma’aikata ta hanyar daidaita muradun kowane ɓangarori.

Mambobin kwamitin sun haɗa da Usman Bala Muhammad a matsayin shugaba, Ibrahim Jibril Fagge (Kwamishinan kuɗi), Musa Suleman Shanono (Kwamishinan kasafi da tsare-tsare), Baba Halilu Dantiye (Kwamishinan yaɗa labarai), da Baffa Sani Gaya.

Sauran su ne Farfesa Aliyu Isa Aliyu, Salahudeen Habib Isa, Ibrahim I. Boyi, Ibrahim Muhammad Kabara, Mustapha Nuraddeen Muhammad, Abdulkadir Abdussalam, Umar Muhammad Jalo, Hassan Salisu Kofar Mata da Yahaya Umar.

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka