Gwamnatin Kano ta kama jabun magunguna na N300m

Kwamitin Kare Masu Amfani da Kayayyaki na Jihar Kano, ya kama jabun magunguna na kimanin kudade N300m a daren ranar Talata.

Gwamnatin Kano ta kama jabun magunguna na N300m

Magunguna

Hukumar Kare Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano ta kama jabun magunguna na kimanin Naira miliyan 300  a daren ranar Talata.

Mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ya ce wani dan kishin jihar ne ya fallasa wani mutum da ke hada jabun magungunan a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi (Sabon Gari) a birnin Kano.

Dan Agundi, wanda ya samu wakilcin mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan KAROTA Nasiru Usman Na’ibawa, ya ce jami’an sun isa kasuwar da misalin karfe 9:30 na daren Talata, bayan samun labarin.

Ya kara da cewa kwamitin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen fataucin jabun magunguna a jihar.

Na’ibawa, ya yaba wa jama’ar jihar kan yadda suke ba wa kwamitin hadin kai da bayanan abubuwan da ke faruwa a lunguna da sako.

Kazalika, ya roki jama’ar da su ci gaba da ba da bayanan da suka dace don dakile yaduwar laifuka da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi.