Gwamnatin Kano ta karbo bashin N177.4bn daga Faransa domin aikin ruwan sha
Za a gina sabuwar ma’ajiyar ruwa mai daukar lita miliyan 250 a kowace rana a Tamburawa
Gwamnatin Jihar Kano ta samu rancen Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Raya kasar Faransa gina sabbin matatun ruwa a Tamburawa da inganta samar da ruwan sha.
Gwamna Abba ya ce aikin na da nufin inganta hanyoyin samun ruwan sha, duba da karuwar al’ummar jihar cikin hanzari.
Abba ya jaddada mahimmancin aikin, wanda ya ce fuskanci tsaiko sakamakon annobar COVID-19 da sauran kalubale, amma yanzu ana sa ran kammala shi nan da shekaru biyu masu zuwa.
Ya ce za a gudanar da aikin ne a karkashin shirin sake fasalin ruwan birane na kasa, kuma ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya ta ba da tabbacin hakan.
- Hajjin 2025: Kafin alƙalamin N8.5 maniyyata za su biya a Legas
- Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ba ta hannunmu —Hisbah
- Mahaifiyar tsohon shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ta rasu
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Ali Haruna Makoda, yayin wani taron bitar ayyuka na kwanaki biyu da aka gudanar a Kano, wanda ya samu halartar wakilai daga jihohin Filato, Enugu, da Ondo.
Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, Garba Ahmad Bichi, ya bayyana cewa, aikin ya hada da gina sabuwar ma’ajiyar ruwa mai daukar lita miliyan 250 a kowace rana, wanda zai magance matsalar karancin ruwan da ake fama da ita a cikin birnin, sakamakon karuwar al’umma.