Gwamnatin Kano ta mayar wa Jami’ar Yusuf Maitama tsohon sunanta
Majalisar Zartaswar jihar ce, ta ɗauki wannan matakin bayan wani taro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a ranar Juma’a.
Gwamnatin Jihar Kano ta mayar wa Jami’ar Yusuf Maitama Sule tsohon sunanta na Jami’ar Northwest.
Majalisar Zartaswar jihar ce, ta ɗauki wannan matakin bayan wani taro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a ranar Juma’a.
- An kuɓutar da ’yar shekara 4 daga hannun mai garkuwa da mutane a Kano
- Gidauniyar Daily Trust ta horas da ’yan jarida kan binciken ƙwaƙwaf a Kaduna
Ana iya tuna cewa, a watan Yulin 2017 tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sauya sunan jami’ar zuwa Yusuf Maitama Sule University, domin karrama marigayi Ɗan Masanin Kano, Yusuf Maitama Sule
“Saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Jihar Kano da Arewa har ma da Najeriya gaba ɗaya.”
Sai dai hukuncin sauya sunan Jami’ar bai yi wa wasu s jihar daɗi ba, ciki har ɗaliban Jami’ar.
Sai dai a wannna karon da gwamnatin jam’iyyar NNPP ke mulki a jihar, ta ɗauki matakin dawo da tsohon sunan Jami’ar.
Sunan Jami’ar na Northwest University ya samo asali ne a lokacin tsohon jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, bayan ƙirƙiro ta a lokacin mulkinsa.