Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero daga fadar Nassarawa
Gwamnatin ta ce akwai buƙatar a mutunta doka, saboda ita ce ta cire Sarkin daga kujerarsa.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Jihar Kano, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗauki mataki na cire Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, daga Fadar Nassarawa, wanda ta ce zamansa na haddasa tashin hankali a jihar.
Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, ya yi wannan kira.
- Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman
- Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Fadar Gwamnatin Kano yayin rabon kayan tallafi da ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tarauni, Hon. Kabiru Dahiru Sule, ya bayar.
Ya zargi wasu mutane na amfani da zaman Aminu Ado a fadar Nasarawa don cimma muradun kansu da kuma haddasa rikici a Kano.
“Muna kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya cire Sarkin da ya naɗa ya kuma ajiye shi a maƙabarta,” in ji Gwarzo.
“Mutanen Kano, musamman matasa, sun gaji da wannan abun kunya.
“Abun mamaki ne a ce a dimokuraɗiyya ana tura jami’an tsaro suna harba wa masu zanga-zangar lumana barkonon tsohuwa, wasu rahotanni ma suna cewa an yi amfani da harsasai na gaske.
“Da yamma, motocin sojoji sun yi sintiri a cikin gari, har ma sun tsaya a kofar gidana. Amma muna so mu bayyana cewa ba za a razana mu ba.
“Wannan dimokuraɗiyya ce, kuma dole ne a mutunta ta, ko ana so ko ba a so. Muna goyon bayan matasan da suka fito domin bayyana damuwarsu.
“Shugaban ƙasa ya ɗauke Sarkin da ya naɗa, ya kai shi jiharsa. Kano tuni tana da Sarki, kuma wannan Sarki shi ne Muhammadu Sanusi II,” in ji shi.
“A yau, ko kai waye, ko da kai ne ‘Sarkin Duniya,’ ba za ka iya naɗa Sarki a Kano ba sai dai idan kai ne Gwamna Abba Kabir Yusuf.”
Gwarzo ya jaddada cewar zaman Aminu Ado a fadar Nasarawa wata maƙarƙashiya ce don hana gwamnatin jihar gudanar da mulki yadda ya kamata.
Ya kuma soki amfani yadda jami’an tsaro ke amfani da ƙarfi a kan masu zanga-zanga, inda ya ce ‘yancin yin zanga-zangar lumana haƙƙi ne a dimokuraɗiyya.
Ya bayyana cewa mutanen Kano suna da haƙƙin neman a cire Aminu Ado Bayero, kuma ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ɗauki mataki cikin gaggawa domin wanzuwar zaman lafiya.
Gwamnatin Kano, ta kuma jaddada cewa doka ce ta tabbatar da naɗin tsohon sarki, kuma doka ce ta dawo da Muhammadu Sanusi II, wanda ta ce dole ne a mutunta doka kuma a bi ta yadda ya kamata.