Gwamnatin Kano ta raba wa waɗanda gobara ta shafa tallafin N12.7m
Gwamnan ya bayar da tallafin ne domin rage wa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗi.
Gwamnatin Jihar Kano, ta raba wa mutum 281 da gobara ta shafa a jihar Naira miliyan 12.7.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Majalisar Zartarwa, Alhaji Adda’u Kutama, ya wakilta, ya ce kuɗin na nufin taimaka wa mutanen da abin ya shafa don rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.
- HOTUNA: Bikin baje kolin al’adun Jihar Filato
- Rikicin ’yan Najeriya da wasu ƙasahe a Soshiyal Midiya a 2024
Ya kuma buƙaci mutanen da su yi amfani da kuɗin yadda ya dace.
Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Alhaji Isyaku Kubarachi, ya gode wa gwamnan bisa wannan tallafi.
Ya bayyana cewa waɗanda abin ya shafa sun yi asarar dukiyoyinsu a gobarar da ta auku ranar 3 ga watan Disamba, 2023, a kasuwanni biyu — Kasuwar ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Dala da kuma Kasuwar Bakin Kasuwar Asibiti da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo.
A cewar Kubarachi, mutum 57 daga Kasuwar ‘Yan Katako da ke Dala da kuma mutum 224 daga Kasuwar Bakin Asibiti da ke Gwarzo sun amfana da tallafin.
Ya ce hukumar ta gudanar da bincike kan asarar da suka yi da kuma ta kai wa gwamnati rahoto domin ɗaukar matakin tallafi.
Kubarachi, ya yaba wa ƙoƙarin gwamnan wajen inganta jihar cikin ƙasa da shekara biyu.
Ya kuma shawarci mazauna jihar, musamman mata masu amfani da itace da gawayi a lokacin damina, su riƙa kula da wuta.
Har ila yau, ya shawarci jama’a su kashe kayan wutar lantarki kafin fita daga gida ko kafin kwanciya barci don kauce wa gobara.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala, Alhaji Suraj Imam, ya gode wa gwamnatin saboda taimakon da ta bai wa waɗanda gobarar ta shafa.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana, Malam Yusuf Muhammad, ya gode wa gwamnatin a madadin sauran mutanen da suka amfana, inda ya ce za su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata.