Gwamnatin Kano ta rufe ofishin lauyan Shekarau

Lauyan ya ce jami’an gwamanti da ’yan sanda sun kulle shi a cikin ofishin nasa tare da ma’aikatansa

Gwamnatin Kano ta rufe ofishin lauyan Shekarau

Rahotanni daga Kano sun bayyana cewa wasu jami’an gwamnatin jihar tare da ’yan sanda sun rufe ofishin lauyan tsagin Shekarau a jam’iyyar APC na jihar, Mista Nureini Jimoh (SAN), da ke Lamba 16c kan titin Murtala Mohammed, a Jihar.

Idan ba a manta ba Mista Jimoh, shi ne lauyan da ya jagorancin nasarar tsagin Sanata Ibrahim Shekarau kan bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shari’ar takaddamar shugabancin jam’iyyar APC a Jihar.

Lauyan ya tabbatar da rufe ginin da ofishin nasa ke ciki ga manema labarai.

Ya ce jami’an gwamnatin sun rufe shi a cikin ofishin tare da wasu ma’aikatansa da kuma wasu mutane.

Cikakken bayani na tafe…