Gwamnatin Kano ta rufe shagon Nagwale mai maganin gargajiya

Hukumar ta umarci wanda ake zargin da ya bayar da sakon neman afuwa a rubuce da kuma bidiyo da sauti, wanda za a yi amfani da shi a matsayin hujja a kansa a nan gaba

Gwamnatin Kano ta rufe shagon Nagwale mai maganin gargajiya

Gwamnatin Kano ta rufe ofishin wani fitaccen mai maganin gargajiya mai suna Nagwale bisa zargin amfani da kananan yara da kuma yin batsa a yayin tallace-tallacen maganin kara kuzarin saduwar aure.

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta ce ta rufe shagon Nagwale ne sakamakon yawaitar korafe-korafen jama’a a kan tallace-tallacen magungunan kamfanin wadanda suke dauke da kalaman da ba su dace ba.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana cewa shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ne ya bayar da umarnin rufe shagon tare da gayyato shugaban kamfanin domin ya amsa tambayoyi kan zarge-zargen.

Daraktan Kula da Da’a na hukumar, Alhaji Zakari Garun Babba, ya bayyana ce salon tallar magungunan Nagwale da kuma amfani da kananan yara wajen yin su, sun saba wa dokokin hukumar.

Da yake gargadin daukar mataki mai tsauri kan masu kunnen kashi, daraktan ya ce, “Ya zama wajibi masu sayarwa da masu tallata irin wadannan abubuwa su sani cewa hukuma ba za ta taba lamuntar amfani da kananan yara ko kuma yin fitsara da sunan tallace-tallace ba.”

Sanarwar da hukumar ta fitar ta bayyana cewa wanda ake zargi ya amsa kuskurensa a gaban hukumar kuma ya nefi afuwar al’ummar Jihar Kano.

A matsayin horo, hukumar ta umarce shi da ya bayar da sakon amsa laifi da neman afuwa a rubuce da bidiyo da kuma sauti, wanda za a yi amfani da shi a matsayin hujja a kansa, idan ya sake a nan gaba.

Da take jaddada aniyarta ta kare kananan yara daga cin zarafi, hukumar ta nanata cewa doka ta ba ta ikon sanya ido a kan ayyukan masu maganin gargajiya, musamman a tallace-tallacen domin tabbatar da tsafta a cikin lamarin.