Gwamnatin Kano ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu

Gwamnatin ta ce wasu daga cikinsu ba su da yanayin da ya kamata mara lafiya ya kwanta a ciki

Gwamnatin Kano ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu a Jihar saboda kin bin wasu dokokinta.

Shugaban Hukumar Da ke kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu a Jihar (PHIMA), Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad ne ya bayyana hakan a lokacin da yake rufe asibitocin da yammacin Asabar.

Farfesa Salisu ya bayyana cewa Hukumarsu ta rufe Asibitin Family Diagnosis Center da ke Kano titin Court Road a unguwar Gyadi-Gyadi ne saboda canza suna da wuri da asibitin ya yi ba bisa ka’ida ba.

A cewarsa a baya sunan asibitin shi ne Al-Sultan Diagnostic Laboratory, amma sai ga shi ya canza sunansa da wurin zamansa ba tare da sanar da hukumar ba.

Haka kuma ya kara wasu ayyuka a kan wanda aka yarje masa ya rika gudanarwa.

“Lokacin da muka je duba asibitin sai muka iske cewa sun ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da saninmu ba. Mun lura cewa ayyukan da suke gudanarwa ba wai duba marasa lafiya kadai ba har da wasu ayyukan da ba mu yi musu rajistarsu ba. Haka kuma har yanzu ba su sanya wasu kayayyakin da ya kamata a ce sun sanya ba.”

Shugaba ya kara da cewa hakan ya sa hukumar ta rufe asibitin, kuma zai ci gaba da kasancewarsa a rufe har sai sun cika kaidojin hukumar da suka hada da samar da isassun ma’aikata da kuma tabbatar da ko ya dace su gudanar da wasu ayyukan ko kuma a’a.

“Idan har suka gaza cika wadannan ka’idojin ba za mu taba bude asibitin ba,” in ji shi.

A wani ci gaban kuma, hukumar ta rufe wasu asibitoci biyu da suka hada da Rich Clinic da Choice Clinics saboda karya dokar Hukumar wajen tafiyar da su.

Farfesa Salisu Ibrahim ya ce asibitin Choice yana rigima ne da wani asibiti da suka hada gini guda wanda kuma suka gano suna ayyukansu ba bisa ka’ida ba.

“Hukumarmu ta soke rajistarsu sannan ta ba su umarnin su canza wani wurin wanda kuma sai Hukumar ta yarje musu. Daya daga cikin asibitocin sun bi umarninmu yayin da shi Asibitin Choice ya bijire wa umarninmu ya kuma ci gaba da gudanar da ayyukansa.

“Lokacin da muka je mun samu akwai wata mara lafiya a kwance hakan ya sa muka saurara har zuwa lokacin da za a sallame ta. Amma dai mun rufe musu tiyatarsu.

“Mun kuma ba su wa’adin makonni biyu su dakatar da ayyukansu amma suka yi kunnen uwar- shegu da umarninmu. Lokacin da muka je, mun rufe asibitin saboda mun samu ba su da likita, babu mai bayar da magani babu wasu ma’aikatan da suka zama dole a harkar kula da lafiya. Ma’aikata biyu kawai suke da su; daga malamar jinya da kuma mai shara.”

Da yake magana game da asibitin Rich kuwa, Shugaban hukumar ya ce dakunan asibitin ba su dace a ce za a ga marasa lafiya a ciki ba ballantana a yi batun kwantar da su a ciki saboda babu iska a ciki mai shiga da fita a cikinsu.