Gwamnatin Kano ta sanar da ranakun komawa makarantu
An tanadi hukunci ga ɗaliban da suka gaza komawa makarantunsu a kan lokaci.
Gwamnatin Jihar Kano, ta ayyana ranakun 5 da 6 ga watan Janairu, 2025 a matsayin ranakun da ɗalibai za su koma makarantu, domin fara zangon karatu na biyu na shekarar 2024/2025.
Gwamnatin, ta bayyana cewa dukkanin makarantun kwana, na gwamnati da masu zaman kansu, za su koma ranar Lahadi, 5 ga Janairu, 2025.
- Matashi ya shiga hannu kan sace yaro ɗan shekara 2 a Kano
- Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza
Makarantun jeka-ka-dawo kuma za su fara komawa ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025.
A wata sanarwa da Balarabe Abdullahi Kiru, Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, ya fitar, an yi kira ga iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma a kan lokaci.
Sanarwar ta gargaɗi cewa ɗaliban da suka kasa komawa a kan lokaci za su fuskanci hukunci.
Kakakin Ma’aikatar Ilimi, Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce gwamnati na ƙoƙarin inganta ilimi tare da samar da yanayi mai kyau da zai taimaka wa ɗalibai su yi nasara.
Sanarwar ta kuma yi fatan alheri ga malamai da ɗalibai yayin fara zangon karatu na biyu.
Ya bayyana cewa za a sa ido akai-akai domin tabbatar da cewa malamai da ma’aikata suna aiki yadda ya kamata.