Gwamnatin Kano ta sanya dokar hana fita
Gwamnatin Kano ta ce sanya dokar hana fitar ta zama dole, saboda dalilan tsaro
Wani jami’in dan sandan Najeriya
Gwamnatin Jihar Kano ta sanya dokar hana zirga zirga a Jihar Kano daga safe zuwa yamma.
Kwamishinan Watsa Labarai, Muhammad Garba ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano, cewa sanya dokar ya zama dole saboda guje wa karya doka da oda duba da irin damuwar da aka shiga a lokacin tattara salamakon zaben gwamnan jihar.
- Abba Kabir Yusuf na NNPP ya zama zababben Gwamnan Kano
- NAJERIYA A YAU: Ko Tasirin Jam’iyyar NNPP Da LP Zai Wanzu A Najeriya?
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa dan takarar gwamna a Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ne ya lashe zabeng gwamnan jihar.
Mataimakin gwamna mai ci, Nasir Yusuf Gawuna, ya zo na biyu, a zaben, wanda kafin sanar da sakamakonsa aka yi ta jira da kananan maganganu.