Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita 

Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashe-tashen hankula a jihar.

Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita 

Gwamnatin Jihar Kano, ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya biyo bayan zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa tashin hankali a ranar Alhamis.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye ne, ya sanar da hakan a daren Asabar a madadin Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf.

Al’ummar jihar za su iya gudanar da harkokinsu daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 2 na rana, wanda zai fara daga Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024.

Gwamnatin ta ce tana bibiyar yanayin tsaro kuma za ta ke bayar da rahoto kan yadda dokar za ta ke ci gaba da aiki.

Dantiye, ya ce gwamnatin jihar ta nuna alhininta ga mutanen da suka rasu da waɗanda suka jikkata sakamakon rikicin da ya ɓarke yayin zanga-zangar #EndBadGovernance.

Ya kuma yi wa waɗanda suka rasa ‘yan uwansu da dukiyoyinsu jaje, inda ya yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka samu raunuka.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS