Gwamnatin Kano ta rushe Jami’ar Sa’adatu Rimi
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe hukumar gudanarwar jami’ar nan take
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya soke Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso, ya mayar da ita kwalejin ilimi.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Baba Ɗantiye, ya sanar cewa, “Gwamna ya rushe hukumar gudanarwar jami’ar nan take”, ya mayar da ita tsohon matsayinta na Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi.
“Ya umarci shugaban rusasshiyar jami’ar da ya mika ragamar jagoranci ga mataimakinsa mafi girman matsayi, daga bisani gwamantin jihar za ta sanar da mataki na gaba.”
Baba Ɗantiye ya ce Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da mayar da Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa tsohon matsayinta na kwalejin ilimi ne a ƙoƙarinta na inganta fannin ilimin gaba da sakandare a jihar.
- Gwamnatin Kano ta ayyana Litinin hutun Ranar Takutaha
- NAJERIYA A YAU: Turka-Turkar Da Ta Dabaibaye Zaben Jihar Edo
Ya bayyana cewar an ɗauki matakin ne bayan samun rahoton kwamitin da gwamnatin ta kafa domin lalubo hanyoyin bunkasa harkokin ilimi da kuma tattaunawa da ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki.
Dalilin rushe Jami’ar Sa’adatu Rimi
A cewarsa, an gano cewa tun da farko akwai illa a ɗaga darajar Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi zuwa jami’a, la’akari da “kasancewarta a mashigar garin Kano inda dalibai da dama daga wajen birnin suke karatu.
“Hakan na haifar da barazanar rasa ƙwarrarrun malamai, bambancin albashi da kuma matsalolin gudanar da ita cikin inganci.
“Sannan Majalisar Zartarwa ta lura cewa jihohi da dama a faɗin Najeriya sun ci gaba da gudanar da kwalejojin iliminsu ba tare da wata matsala ba, ƙarƙashin tsarin bayar da takardun shaidar kwarewar malanta da kuma shaidar digiri, ba tare da kwalejojin sun koma jami’o’i ba.”
Makomar Ɗalibai
A cewarsa, soke matsayin jami’ar “ba zai shafi karatun ɗalibanta ba, kuma kwalejin zai kasance mai bayar da shaidar kammala karatun digiri.
“Sannan zai ci gaba da gudanar da darussa a wasu fannonin,” da ba na ilimi ba.
Ana iya tuna cewa tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ce ta daga darajar kwalejin ilimin na Sa’adatu Rimi mallakar gwamnatin jihar zuwa jami’ar ilmi.