Gwamnatin Kano ta yi garambawul a kulob din Kano Pillars

Gwamnatin Jihar Kano ta rushe hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tare da  nada sabuwar hukumar gudanarwa wadda za ta ci gaba da tafiyar da harkokin kungiyar ba tare da bata wani lokaci ba.A cikin wata sanarwa wadda  daraktan yada labarai na gwamnan jihar   Malam Halilu Baba  dantiye ya sanya wa hannu,  an […]

Gwamnatin Kano ta yi garambawul a kulob din Kano Pillars
Gwamnatin Kano ta yi garambawul a kulob din Kano Pillars

Gwamnatin Jihar Kano ta rushe hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tare da  nada sabuwar hukumar gudanarwa wadda za ta ci gaba da tafiyar da harkokin kungiyar ba tare da bata wani lokaci ba.
A cikin wata sanarwa wadda  daraktan yada labarai na gwamnan jihar   Malam Halilu Baba  dantiye ya sanya wa hannu,  an bayyana cewa gwamnan jihar  Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da rushe hukumar gudanarwar kungiyar tare da nada sabuwar hukuma wadda za ta ja ragamar kungiyar nan take.
Sanarwar ta ce  an nada Alhaji Kabiru Baita a matsayin sabon shugaban kungiyar sai Alhaji Abba Dambazau da Malam Naziru Wapa da Garba Muhammad Nawamba da kuma Alhaji Hassan Gwarzo a matsayin membobi a hukumar, inda kuma aka nada wakili daga hukumar wasanni ta jihar Kano a matsayin sakataren hukumar gudanarwar.
Haka kuma babban kocin kungiyar watau Mista Emordi da Janar Manajan kungiyar  duk  an sallame su tare da yin godiya a gare su bisa kokarin da suka yin a bunkasa kungiyar.
Ita dai Kano Pillars ita  ke rike da kambun zakarun gasar rukunin Najeriya na kamfanin sadarwar Glo amma a halin yanzu  tana matsayi na 9 ne a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar bayan ta hada maki 27 a wasanni 19.   Sai  dai masu yin sharhi kan al’amuran  wasanni sun bayyana cewa nada sabuwar hukumar kula da kungiyar shi ne abu mafi dacewa idan aka dubi irin halin da kungiyar ke ciki a yau.
Wakilinmu ya samu ganawa da sabon shugaban kungiyar ta Kano Pillars Alhaji Kabiru Baita ,inda ya ce ce zai jagoranci kungiyar bisa kwarewar da yake da ita ta yadda za ta kasance daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa da ake da su a Nijeria da ma a Afirka baki daya.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja