Gwamnatin Kano ta yi martani kan ɗaga tuta a Fadar Nassarawa
Gwamnatin Kano ta yi watsi da batun ɗaga tutar masarauta da aka yi a gidan sarki na Nassarawa, wurin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune. Gwamnatin ta bayyana ɗaga tutar a matsayin wani kokari na jan hankalin jama’a kawai. An dakatar da dagaci da kansila kan satar taransifoma a Gombe Mutum […]
Gwamnatin Kano ta yi watsi da batun ɗaga tutar masarauta da aka yi a gidan sarki na Nassarawa, wurin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune.
Gwamnatin ta bayyana ɗaga tutar a matsayin wani kokari na jan hankalin jama’a kawai.
- An dakatar da dagaci da kansila kan satar taransifoma a Gombe
- Mutum biyu sun shiga hannu kan zargin sace mahaifiyar Rarara
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya yi fatali da batun ɗaga tuta a Fadar Nassarawar, inda ya ce hakan wani yunƙuri ne na jan hankalin al’umma.
Ya shaida wa manema labarai cewar, “hakan wani yunƙuri ne na jan hankalin al’umma amma babu shakku ko tantamar cewar Sanusi ne Sarkin Kano.”
Tutar, wata alama ce ta iko dake nuni da cewar Sarki na nan, a kullum ana ɗaga ta da misalin karfi 6 na safe a kuma sauketa da 6 na yamma.
Duk lokacin da sarki ba ya cikin fada ko ya yi balaguro tutar za ta kasance a sauke.
Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Alhamis ce aka ɗaga tutar da misalin karfe 6 na safiya a Fadar Nassarawa, abin da ya haifar da kace-nace da ma raɗe-raɗi.
Kowanne daga cikin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II na ikirarin shi ne Sarkin Kano kuma suna ci gaba da aiwatar da ayyukan sarauta.
An ɗaga irin wannan tuta a Fadar Gidan Rumfa, inda Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ke zaune.
Tun dai a ranar 23 ga Mayun 2024 ne, Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya sa hannu a kan sabuwar Dokar Masarautu ta Shekarar 2024 wacce Majalisar Dokokin Jihar ta amince da ita.
Wannan dokar dai ta soke sarakuna 5 masu daraja ta daya da suka hada da Kano da Bichi da Rano da Karaye da Gaya da Bichi da kuma duk wasu nade-nade da aka yi kafin dokar.
Haka kuma Gwamnan ya sake dawo da tubabben Sarki na 14 Malam Muhammadu Sanusi II, sai dai an kalubalanci wannan yunkuri na gwamnati a kotu, inda ake neman dawo da Aminu Ado Bayero a kan kujerarsa duba da cewa ba ya garin yayin da aka tube shi, kuma ba a tuhume shi da aikata laifi ba kafin a tube shi.
Hotunan yadda aka daga tutar a Fadar Nassarawa