Gwamnatin Kano za ta aurar da mata 1,111 ciki har da Kiristoci

Babban Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya ce hukumar ta fara shirye-shiryen aurar da mata 1,111 ciki har da Kiristoci 50 nan ba da dadewa ba. Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana haka ne a taronsa da ‘yan jarida a shekaranjiya Laraba, inda ya ce sun fito da sababbin tsare-tsare don shirin […]

Gwamnatin Kano za ta aurar da mata 1,111 ciki har da Kiristoci
Gwamnatin Kano za ta aurar da mata 1,111 ciki har da Kiristoci

Babban Kwamandan Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya ce hukumar ta fara shirye-shiryen aurar da mata 1,111 ciki har da Kiristoci 50 nan ba da dadewa ba.
Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana haka ne a taronsa da ‘yan jarida a shekaranjiya Laraba, inda ya ce sun fito da sababbin tsare-tsare don shirin aurar da matan karo na hudu ya cimma nasara.
“A yanzu za mu rika yin rajistar masu neman aure maza da mata ta hanyar intanet don saukake musu zirga-zirgar zuwa hedikwatar hukumar. Kuma mun samar da na’urori na zamani don tantance lafiyar masu neman auren, ciki akwai wadda za ta gano mace mai ciki koda na wata daya ne, saboda mun taba samu wata da ta yaudare mu ta kawo fitsarin ’yar uwarta aka auna a matsayin nata, bayan ta tare aka gano tana da ciki na wata shida,” inji shi.
A cewar Kwamandan “A wannan karon mun ware wa ’yan uwanmu Kiristoci gurbi 50 daga cikin 1,111, inda muka bukaci su kawo angwaye da amarensu mu ba su tallafin. Kuma za mu ba su dama su je su daura aurensu a coci kamar yadda suka saba. Mun yi haka ne don nuna musu cewa su ma ’yan uwanmu ne, yadda ba mu son ’ya’yanmu su shiga karuwanci haka su ma ba mu son ganinsu a cikin harkar karuwancin,” inji shi.