Gwamnatin Kano za ta ba mata bashin Naira biliyan biyu

A shirye-shiryenta na tallafa wa mata da matasa, Gwamnatin Jihar Kano tare da hadin kan Bankin Kasuwanci ta shirya bitar wayar da kai ga daruruwan matan jihar akan karbar bashin Naira biliyan biyu. Mashawarcin Gwamnan Kano akan harkokin kasuwanci Muhamamd Jamu wanda ya yi jawabi a wajen taron ya bayyana cewa duk da cewa shirin […]

Gwamnatin Kano za ta ba mata bashin Naira biliyan biyu

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar KanoA shirye-shiryenta na tallafa wa mata da matasa, Gwamnatin Jihar Kano tare da hadin kan Bankin Kasuwanci ta shirya bitar wayar da kai ga daruruwan matan jihar akan karbar bashin Naira biliyan biyu.

Mashawarcin Gwamnan Kano akan harkokin kasuwanci Muhamamd Jamu wanda ya yi jawabi a wajen taron ya bayyana cewa duk da cewa shirin ba wai an kebence shi ga mata kawai ba, amma ana tunanin za su amfana da kashi 60 cikin 100 na asusun. “A lokacin bitar farko mun samu maza kimanin 700 da mata 21. Saboda haka muka yi tunanin mu sake wannan bitar saboda mata su amfana daga shirin. Idan har matan suka cika sharuddan karbar bashin za su sami kashi 60 na asusun. Wasu za su sami miliyan 10, wasu miliyan biyar, wasu miliyan biyu, wasu kuma daya ya danganta da irin tsarin kasuwancin da mutum yake gudanarwa. Sai dai ba za mu iya bayyana yawan mutanen da su amfana daga shirin ba” Inji shi.
Jamu ya bayyana cewa zuwa yanzu fiye da mutane 400 ne suka cika sharuddan karbar bashin, haka kuma suna tsammanin wasu takardun mutanen na gaba. Ya kuma kara da cewa za a fara bayar da bashin kudin ne a watan Nuwamba zuwa Disambar wannan shekara.
Sannan mashawacin Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin Kano ta bayar da gudunmawar Naira biliyan daya yayin da shi ma Bankin Kasuwanci ya bayar da Naira biliyan daya. Haka kuma karin kudin da mutum zai biya daga kashi biyar ne zuwa shida cikin 100, kasancewar gwamnati ta ce ba ta bukatar kudin ruwa.
A jawabin Mataimakin Gwaman Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yaba wa matan jihar game da shiga da suke yi cikin duk wasu shirye-shiryen gwamnati na tallafa musu, don haka ya nemi su yi amfani da kudin bisa tsari domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.