Gwamnatin Kano za ta fara ba da rigakafin cutar shan-inna a cikin motocin haya
Gwamnatin Jihar Kano ta shirya domin fara bai wa yara rigakafin cutar shan-inna a cikin motocin haya idan sun shigo jihar daga wata jihar domin magance yaduwar cutar.Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Kabiru Ibrahim Getso ne ya sanar da haka bayan tattaunawa da wani kwamitin na musamman kan rigakafin cutar shan-inna.Ya ce sun dauki wannan […]
Gwamnatin Jihar Kano ta shirya domin fara bai wa yara rigakafin cutar shan-inna a cikin motocin haya idan sun shigo jihar daga wata jihar domin magance yaduwar cutar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Kabiru Ibrahim Getso ne ya sanar da haka bayan tattaunawa da wani kwamitin na musamman kan rigakafin cutar shan-inna.
Ya ce sun dauki wannan matakin ne saboda barkewar da cutar ta yi a Jihar Borno, sannan ya ce yin rigakafin a cikin motocin hayan yana daya daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar ta dauka domin magance yaduwar cutar. “Gwamnatin Jiha ta riga ta dauki duk wani mataki da ya dace domin samun nasara, daya daga cikin wadannan matakai shi ne duba kowace mota da ta shigo jihar daga wata Jiha kafin fasinjoji su sauka a cikin garin Kano.