Gwamnatin Kano za ta fara kai samame rumbunan da aka ɓoye kayan abinci
Duk wani dan kasuwa da ke barazanar rufe shago yana tallafa wa masu ɓoye kayan masarufi ne.
Gwamnatin Jihar Kano ta yi barazanar fara kai samame rumbuna da shagunan da ake zargin ’yan kasuwa na ɓoye kayan abinci da nufin samun riba mai yawa a lokacin tsadar kayan.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta Kanon (PCACC) ce ta yi wannan gargadin ga ‘yan kasuwar da ake zargi da ɓoye kayan abinci da su daina.
Hukumar ta ce bayan korafe-korafen da ta karɓa daga mutane daban-daban ta umarci jami’anta su fara bincike wuraren da ake zargin an makare manyan sito-sito da kayan abinci.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce sun gano cewar boye kayan na daga cikin abubuwan da suke kara tsadar kayan masarufi a Kano, inda ya ce duk mutumin da suka kama to zai ɗanɗana kuɗarsa.
“Abin mamaki da takaici shi ne yanzu haka ana sayar da buhun sukari a kan sama da Naira 73000.
“Ko a jiya na ziyarci wasu kamfanonin shinkafa a Kano, inda muka gano cewa farashin duk buhu mai nauyin kilo 50 ya kai 58000,” in ji Muhyi.
Yayin da yake kira ga masu ɓoye kayan abinci da su daina ko kuma a gurfanar da su gaban kuliya, Muhuyi ya ce wani bangare na aikin hukumar shi ne yaƙi da cin hanci da rashawa wanda daga cikin abubuwan da ke assasa matsalar akwai hauhawar farashin kayayyaki.
Rimin Gado ya ce, bai kamata a ɗora alhakin lamarin a kan matsalar canjin kudaden waje kaɗai ba, domin kuwa a cikin gida ake samar da wasu kayayyaki, don haka babu hujjar hauhawar farashin kayayyaki, yana mai cewa, wasu na yin amfani da wannan lamarin don kara samun riba.
A cewarsa, sashe na 40 na kundin dokokin hukumar ya ba su damar yin gwanjon kayayyakin da suka kama a hannun masu ɓoye kayayyakin buƙata.
Dangane da barazanar da ’yan kasuwa suka yi ta rufe kasuwanci saboda tashin farashin kayan abinci, Rimin Gado ya ce duk wani dan kasuwa da ke barazanar rufe shago yana tallafa wa masu ɓoye kayan masarufi ne kuma gwamnatin jihar ba za ta nade hannunta ba alhali lamarin yana kara tabarbarewa.
Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kai rahoton duk ‘yan kasuwar da ke ɓoye kayayyakin abinci, yana mai cewa hukumar za ta zage damtse musamman ganin yadda azumin watan Ramadan ya gabato domin rage musu raɗaɗin kuncin rayuwa.
A wata ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi da ‘yan kasuwa a ranar Litinin da ta gabata, ya nuna damuwarsa kan yadda ake fama da yunwa gami da tashin farashin kayayyakin masarufi a Kano, inda ya sha alwashin miƙa koke ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin kawo wa jama’a tallafi.
Ana dai ta zarge-zarge cewa manyan ’yan kasuwa na boye kayan masarufi har sai ya yi tsada su fito da shi su sayar, wani abu da ake ganin yana taimakawa wajen kara dagula lamarin tsadar kayan na masarufi a Najeriya.
‘Yan kasuwa dai a Kano da ma Najeriya na musanta zarge-zargen da ake yi musu, inda ko a makon da ya gabata sai da gamayyar kungiyar ‘yan kasuwa a birnin Kano ta yi barazanar rufe kasuwanci saboda tsadar kayayyaki.