Gwamnatin Kano za ta fitar da kundi don magance ɗumamar yanayi
Gwamnatin ta ce samar da kundin ya zama tilas duba da yadda ɗumamar yanayi ke cutar da al’umma a jihar.
Hukumar Kula da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, ta ce nan ba da jimawa ba za ta fitar da wani kundi da zai zama doka a kan abin da ya shafi ɗumamar yanayi a jihar.
Shugaban hukumar, Muhammad S. Khalil, ya bayyana cewa sauyin yanayi ya shafi kowane fanni na rayuwar ɗan Adam, wanda hakan ne ya sa hukumar za ta kafa dokar da za ta magance matsalar.
Ya kuma ƙara da cewa duba da ɗumamar yanayi ta ke da duniya, ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ta nemi kowace ƙasa ta samar da dokar da za ta magance matsalar.
“A yanzu haka hankalin duniya yana kan wannan al’amari na ɗumamar yanayi.”
Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce dole ne kowace ƙasa ta samar da tsari na musamman domin shawo kan matsalarta.
Ta ce ba za a iya magance matsalar ba har sai an samar da wani tsari na kowace ƙasa ko kuma jiha wanda zai duba abin da wannan jihar ta keɓanta da shi wanda kuma zai zo da irin dabarun da za bi a magance matsalar.
A cewarsa: “Jihar Legas ce ta fara yin wannan doka a faɗin ƙasar nan.
“Muna so Jihar Kano ta bayanta. A watan Fabrairu mun yi irin wannan taron, inda muka kira masana da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen jihar nan da ƙasar nan don mu fitar da wani kundi a kan ɗumamar yanayi a Jihar Kano, inda kuma a yanzu muka yi nasarar fitar da kundin.”
A nasa jawabin masanin muhalli, Dokta Umar Saleh Anka, ya bayyana cewa babu ƙasar da za ta ci gaba sai ta magance matsalar ɗumamar yanayi, musamman ma Jihar Kano da ta fi kowacce jiha yawan al’umma.
“Ita wannan matsalar ta ɗumamar yanayi ta fi damun Jihar Kano saboda yawan al’umma da yawan ababen hawa da jihar ke da shi.
“Lamarin kuma yana shafar lafiyar al’umma da harkokin noma da kiwo.”
Ya ƙara da cewa ba za a iya sanya doka ba tare da an yi mata shimfiɗun da suka dace ba.
A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin da ke kula da Muhalli a Majalisar Dokokin Jihar Kano, ɗan majalisa mai wakiltar Takai, Honorabil Musa Ali Kachako, ya tabbatar da cewa da zarar an kai wannan ƙuduri majalisa za ta sanya masa hannu.
“Kamata ya yi idan an zo da wani abu mutane su tsaya su fahimce shi don gane amfaninsa ga al’umma a maimakon a yi fatali da shi tun da farko. Idan an fahimce shi sai kuma a karɓe shi don amfanin al’umma,” in ji shi.