Gwamnatin Kano za ta kafa kamfanin jirgin sama mallakin jihar

Gwamnan ya ce lokaci ya yi da jihar za ta mallaki kamfanin jirgin sama na ƙashin kanta.

Gwamnatin Kano za ta kafa kamfanin jirgin sama mallakin jihar

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatinsa na kafa kamfanin jirgin sama mallakin jihar, da nufin samar da guraben ayyukan yi ga matuƙa jirgi ’yan asalin jihar.

Gwamnan, ya sanar da wannan shiri ne yayin zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 40, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Kano.

Ya tabbatar da cewa ana sa ran sabon kamfanin jiragen saman zai fara aiki nan da shekara guda mai zuwa.

A cewar gwamnan, babban burin wannan aiki shi ne samar da dama ga matuƙa jirgi ƙwararru ƙarƙashin tallafin jihar, waɗanda suka daɗe suna jiran damar nuna ƙwarewansu.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta bayar da duk wani goyon baya da ake buƙata na kuɗi da kayan aiki domin ganin nasarar shirin.

Hakazalika, Gwamnan ya jinjina wa bajintar da matuƙa jirgin suka nuna, waɗanda gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin horas da su a Kwalejin Horar da Tuƙin Jiragen Sama ta Ƙasar Jordan.

Ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da farfaɗo da ɓangaren sufurin jiragen sama da kuma bai wa matasan jihar damar bayar da tasu gudummawar wajen bunƙasa tattalin arziƙin Kano.

A nasa ɓangaren, Shugaban Ƙungiyar Matuƙa Jirgin Sama ta Jihar Kano, Naziru Ibrahim, ya miƙa sakon godiya ga gwamnan bisa tallafin da ya bayar wajen sabunta lasisin tuƙinsu da ya daɗe da ƙarewa.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta ci gaba da ba su ƙwarin gwiwa wajen samun takardu, waɗanda za su ba su damar tuƙa manyan jiragen kasuwanci a ciki da wajen Najeriya.

Manyan ‘yan bindigar da aka halaka a Arewa maso Yamma

Amfanin lallen gargajiya

Yadda cutar mafitsara ke wa maza kisan mummuke 

Bikin yaye daliban Islamiyya na tatsar iyaye