Gwamnatin Kano za ta kashe biliyan 40 wajen gina gadojin sama da wasu ayyuka

Za a gina gadojin ne a kan kusan Naira biliyan 30

Gwamnatin Kano za ta kashe biliyan 40 wajen gina gadojin sama da wasu ayyuka

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 40 domin aiwatar da wasu manyan ayyuka a fadin Jihar.

Hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Baba Halilu Dantiye, a cikin wata sanarwa ranar Talata.

Sanarwar ta ce daga ciki, za a kashe biliyan 15.9 domin gina gadar kasa a Dan Agundi, sai wata kuma a shataletalen Tal’udu a kan biliyan 14.4.

Baba Dantiye ya kuma ce, “Majalisar ta amince da fitar da Naira biliyan 3.3 ga Ma’aikatar Ayyuka domin ƙara kudin aikin kwatar Jakara zuwa Kwarin Gogau.

“Kazalika, za a kashe biliyan ɗaya da rabi domin gina titi daga Kofar Waika zuwa Unguwar Dabai zuwa ’Yan Kuje da ke Karamar Hukumar Gwale.

“Kazalika, za a kashe biliyan 1.3  domin gina hanya daga Unguwa Uku ’Yan Awaki zuwa Limawa da ke Karamar Hukumar Tarauni, sai miliyan 820 domin karasa aikin titin Kanye zuwa Kabo zuwa Dugabau a Karamar Hukumar Kabo.

“Majalisar ta kuma amince  da fitar da miliyan 802 domin wasu ayyuka da suka hada da mayar da titin Kofar Dawanau zuwa Dandinshe zuwa Kwanar Madugu mai hannu biyu, sai Naira miliyan 454 domin ayyukan gina gadojin masu tsallaka titi a sassan Kano daban-daban, yayin da za a kashe miliyan 420 domin gyara fitilun kan titi a fadin Jihar Kano,” in ji sanarwar.

Kwamishinan ya kuma ce gwamnatin ta amince da kashe miliyan 200 domin biyan kudaden da suka rage a gyara titin Kwanar Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi, sai Naira miliyan 107 domin gyara makarantar kangararrun yara ta Karamar Hukumar Kiru.