Gwamnatin Kano za ta samar da kasuwar magungunan gargajiya
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na samar da kasuwar masu maganin gargajiya da za ta yi gogayya da takwararta ta zamani a wani yunkuri na tsaftacewa, tare da bunkasa harkar gaba daya. Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a wajen taron bita tare da tantance masu sana’ar maganin gargajiya, wanda […]
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na samar da kasuwar masu maganin gargajiya da za ta yi gogayya da takwararta ta zamani a wani yunkuri na tsaftacewa, tare da bunkasa harkar gaba daya.
Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a wajen taron bita tare da tantance masu sana’ar maganin gargajiya, wanda gwamnatin ta shirya don inganta sana’ar.
Gwamnan ya bayyana cewa samar da kasuwar ga masu magungunan gargajiyar zai bayar da dama wajen samun hadin kan masu sana’ar tare da saurin bankado batagari daga cikinsu wanda ke fakewa da sana’ar su yi gabankansu.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa tatance masu maganin abu ne da ya zama dole bisa la’akari da irin muhimmanicn da maganin yake da shi ga al’ummar jihar.
”Kowa ya san yadda alumma suke daukar magungunan gargajiya da muhimmanci, abu ne da ya zama gidan kowa da akwai don haka akwai bukatar a kula da shi don gudun aukawa cikin wasu cutukan abin da ka iya zama daga neman gira a rasa ido,” inji shi.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da shirya irin wannan bitar lokaci zuwa lokaci, don ganin masu maganin sun kara samun kwarewa da gogewa wajen gudanar da sana’arsu.
Mai ba Gwamna shawara kan harkokin magaanin gargajiya Haruna Muhammad Ibnsina ne ya bayyana cewa zuwa yanzu an tantance masu sana’ar maganin gargajiaya kimanin dubu 10 don fitar da bara-gurbi daga harkar.
Wasu daga masu maganin gargajiyar sun bayyana farin cikinsu game da bitar da aka yi musu, inda suka nemi gwamanti da ta sama musu wani tsari da tallafi don bunkasa sana’ar tasu.
A cewar Hajiya Hauwa Sharada mai maganin gargjiya: “Muna sane da yadda gwamnati take bayar da tallafi ga sauran masu sana’o’i to mu ma muna kira gareta da ta dube mu ta kuma tallafa mana”