Gwamnatin Katsina ta ba kulob din Sportlight Naira miliyan 40

Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya amince a bai wa kungiyar wasan kwallon kafa ta Katsina Sportlights zunzurutun Naira miliyan arba’in da dubu casa’in da tara don cigaba da harkokinta na wasanni. Bayanin haka na kunshe ne a wata  sanarwa da aka raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun Babban Mai […]

Gwamnatin Katsina ta ba kulob din Sportlight Naira miliyan 40
Gwamnatin Katsina ta ba kulob din Sportlight Naira miliyan 40

n Gwamnan Katsina, Barista Ibrahim Shehu ShemaGwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya amince a bai wa kungiyar wasan kwallon kafa ta Katsina Sportlights zunzurutun Naira miliyan arba’in da dubu casa’in da tara don cigaba da harkokinta na wasanni. Bayanin haka na kunshe ne a wata  sanarwa da aka raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun Babban Mai ba Gwamna Shawara na musamman a kan kafofin yada labarai, Malam Lawal Ahmad Matazu a makon jiya.  Sanarwar ta ce wadannan kudi da aka mika su ga ma’aikatar matasa da wasanni domin baiwa jami’in da ke kula da wannan kungiya an bayar da su ne domin cigaba da shirye-shiryen kungiyar a zango na biyu na kakar wasa ta bana.
Bayar da wadannan kudi da Gwamna Shema ya yi ga kungiyar na daga cikin kyawawan kudurori da manufofin gwamnati na ciyar da harkokin wasanni gaba a duk fadin jihar.  Malam Lawal ya ce, wannan ne ma ya sa gwamnatin Shema ta yi kokarin kammala ginin babban filin wasa na jihar, wanda aka yi watsi da shi a baya, inda yanzu haka aka kashe wa filin Biliyoyin Naira don ya zama irin na zamani.
“Kamar yadda kowa ya sani, kungiyar wasan kwallon kafa ta Sportlights na kan gaba wajen lashe kofuna da kyautuka a ciki da wajen jiha don haka gwamnati take kokarin cigaba da karfafa musu gwiwa”, inji shi.