Gwamnatin Katsina ta haramta sana’ar POS da cajin waya

Sabuwar dokar zartarwar da Gwamna Raɗɗa ya sanya hannu ta kuma haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a fadin jihar nan take

Gwamnatin Katsina ta haramta sana’ar POS da cajin waya

Injin POS

Gwamnatin Katsina ta haramta gudanar da sana’ar cirar kuɗi ta PoS da cajin waya da kuma haya da babur a yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da Musawa ta Jihar nan take.

Sabuwar dokar zartarwar da Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu ta kuma haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a fadin jihar nan take, a matsayin wani mataki na daƙile ayyukan da ake zargin suna taimaka wa harkokin ’yan bindigar.

Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya sanar cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan ne baya zaman gaggawa da ta yi da shugabannin tsaro da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’adda na amfani da shagunan POS da wuraren canjin waya da kuɗi wajen gudanar da harkokinsu na kuɗaɗe da kiyaye-kirayen waya.

Kazalika ya bayyana cewa haramcin da aka sanya kan sayarwa ko ɗaukar man fetur a jarkoki a jihar na da nufin daƙile yiwuwar isar man fetur ga ’yan ta’adda a maɓoyarsu da ke cikin dazuka.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya ce rahotannin sirri sun nuna cewa safarar mai a cikin cikin mazubai na taimakawa ci gaba da ayyukan ta’addanci, lamarin da ya sa gwamnati ta ɗauki mataki mai tsauri domin katse hanyoyin samar da kayan buƙatun ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Haka kuma, umarnin rufe dukkan cibiyoyin hada-hadar POS da wuraren cajin wayoyi na kasuwanci a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa nan take na da alaƙa da rahoton binciken jami’an tsaro da ya nuna cewa ana amfani da wasu daga cikin cibiyoyin wajen saukaka sadarwa da hada-hadar kudi ga masu aikata laifuka.

“Mahukunta sun yi imanin cewa wannan zai rage wa ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane damar zirga-zirga, kasancewar galibi suna amfani da babura wajen kai-komo tsakanin al’ummomi,” in ji sanarwar.

Gwamna Raɗɗa ya sake jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne babban nauyin da ke kan gwamnatinsa, yana mai tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Gwamnan ya buƙaci al’umma su ba da goyon baya ga ayyukan tsaro da ake gudanarwa ta hanyar bin sabbin umarnin da kuma bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya yi gargadin cewa duk wanda ya karya Dokar Zartarwar zai fuskanci hukunci mai tsauri, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi sassauci ga masu saba wa dokar ba.