Gwamnatin Katsina ta yi watsi da yankin Daura – Salisu Daura

Alhaji Salisu Ado Daura shi ne dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Daura da Sandamu da Mai’aduwa daga Jihar Katsina a tattaunawarsa da manema labarai ciki har da Aminiya ya soki gwamnatin jihar da yin watsi da yankinsa wajen gudanar da ayyukan raya kasa: Aminiya: Lura da yadda ka zo majalisa yaya za ka kwatanta yadda […]

Gwamnatin Katsina ta yi watsi da yankin Daura – Salisu Daura

Alhaji Salisu Ado Daura shi ne dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Daura da Sandamu da Mai’aduwa daga Jihar Katsina a tattaunawarsa da manema labarai ciki har da Aminiya ya soki gwamnatin jihar da yin watsi da yankinsa wajen gudanar da ayyukan raya kasa:

Alhaji Salisu Ado DauraAminiya: Lura da yadda ka zo majalisa yaya za ka kwatanta yadda harkoki ke tafiya a Majalisar Tarayya?
Al’amura suna tafiya yadda suka kamata, duk da cewa ba mu dade a majalisar ba, saboda sai da Kotun koli ta yanke hukunci a watan Disamban 2011, muka je majalisar a ranar 12 ga Janairun 2012. Don haka yanzu shekararmu biyu a majalisar. Kuma ana gudanar da muhawara sosai kuma komai na tafiya daidai, mun fara sabawa da harkokin Majalisar Tarayya muna shiga ana damawa da mu a harkokinta.
Kasancewar wasu abokan takararku ne suka fara zuwa, wanda hakan ya rage tsawon zamanku a majalisar kana ganin wannan ya kawo muku cikas ko rashin cimma nasara a zaman majalisar?
A’a ba haka ba ne. Abin da kawai zan ce kafin mu zo akwai wasu abubuwa da suka faru ba mu nan, kamar shirya taron fadakar da sababbin ’yan Majalisar Tarayya da ba mu samu halarta ba, sai batun rarraba kwamitoci. Lokacin da muka shigo sai aka ce mu haye kan kujerun da wadanda suka gabace mu suke kai. Baya ga haka ba na jin hakan ya shafi gudunmawarmu ga harkokin majalisar.
Me za ka iya cewa shi ne babban gudunmawar da ka bayar a majalisa da kuma jama’ar mazabarka?
To, wannan tambaya ce mai kafa biyu. A lokacin da ake muhawara a majalisa kan wata bukata da sauran al’amura, kada a manta mu 360 ne, don haka ba kowane lokaci ne kowa zai samu damar yin magana kan kowace bukata ba, amma idan aka samu dama sai mutum ya yi magana. Kuma a matakan kwamiti ko yau mun yi taro da Ma’aikatar Ilimi da hukumomin da suke karkashinta, mun fara jiya har zuwa yau, inda muka tattauna kan yadda za su kare kasafin kudinsu, kuma za mu ci gaba har zuwa makon gobe. Don haka a matsayin dan majalisa kakan shiga a dama da kai a matakan kwamitoci da lokutan muhawara a zauren majalisa da sauransu.
Game da abubuwan da muka yi wa mazabarmu, zan iya cewa mun yi dimbin abubuwa, cikin yardar Allah mun ci sa’a, mun samu nasarar kammala kusan dukkan ayyukan da muke gudanarwa. Zai yi wahala a iske aikin da ba mu kammala ba. Idan ka dauki bangaren ilimi ga misali, abin da na fara yi shi ne da na fahimci akwai dimbin wadanda suka kasa kammala sakandare a mazabata, ko suka kammala amma ba su samu kyakkyawar sakamakon da za ta ba su damar zuwa babbar makaranta ba, suna zaune ba su da aikin yi, sai na fara tunanin yadda zan taimaka. Na sanya aka yi shela a yankunan mazabar cewa duk dan sakandaren da bai kammala ba ko jarrabawarsa ba ta yi kyau ba, da ke son gyara takardunsa ya zo ya yi rajistar sunansa. Na samu sama da mutum dubu biyu, sai na bullo da shirin ba su horo na wata hudu, wadanda suka samu nasara muka saya masa fom din WAEC da NECO da NABTEB, na dauki kimanin malamai 70 suka ba su horo a darussa daban-daban na wata hudu a kananan hukumomi uku da ke mazabar. A karshe aka samu dalibai 1,100 suka yi jarrabawar gwaji suka samu nasara, muka saya musu fom din yin jarrabawar WAEC da NABTEB kuma suka samu nasarar jarrabawar da suka yi. Game da ayyukan gine-gine a shekarar 2012 na gina rukunin ajujuwa biyar an kammala su an mika su ga kananan hukumomin, a bara mun kammala wasu ajujuwan ciki har da jerin ajujuwa biyar (blocks) wadanda muka yi a makarantun Islamiyya, ina jin mun kammala ajujuwa 11 da dakin taro a garin Daura da karamin asibiti a karamar Hukumar Mai’aduwa da sauransu. A bangaren ruwan sha a kowace mazabar unguwa na yi musu rijiyar burtsatse akalla daya, wasu biyu wasu ma uku. Akalla na yi bohul kusan 50 a mazabar, sai bohul mai amfani da hasken rana guda uku. Sai taransfomomi guda hudu tare da sanya su da hada su da hanyar wutar lantarki ta kasa. Kuma a kowace karamar hukuma na mazabata na zabi wani gari na sanya musu wutar lantarki na kan hanya mai aiki da hasken rana. A bangaren tallafa wa jama’a kamar daukar nauyin jinyar marasa lafiya da masu matsalolin rayuwa wannan muna taimaka wa dimbin jama’a ba zan iya sanin adadinsu ba.Yanzu haka akwai majinyata biyar da ke kwance a asibiti da nake daukar nauyin jinyarsu. Sannan ina ba da tallafin karo ilimi ga daliban jami’o’i da na manyan kwalejoji da makarantu domin karfafa musu gwiwar yin karatu. Taimako irin na aure ko suna wannan ba a maganarsa.
Umarnin da jam’iyyarku ta APC ta ba wakilanta a majalisa cewa kada su amince da kasafi sai an warware wasu batutuwa da suka shafi kasa ya jawo cece-kuce, me za ka ce kan haka?
Abin bakin ciki shi ne mutane, sun sanya son rai game da wannan umarni da jam’iyyarmu ta bayar, abu ne sananne cewa abubuwa suna faruwa a kasar nan ba daidai ba, musamman a Jihar Ribas. Kowa yana sane da abin da ke faruwa, ba niyyar jam’iyyar ce a ja kafa marar amfani game da amincewa da kasafin ba. Kuma koda za ka ja kafa kan amincewa da kasafi wajibi ne ya zamo kana da dalili, kuma a lokacin akwai dalilan yin hakan, kamar yadda lamarin ke gudana a Jihar Ribas. Kuma ba ya ga wannan akwai wasu ka’idoji da ake cikawa kafin amincewa da kasafi, kamar kasafin wasu hukumomin gwamnati, irin su EFCC da CBN da sauransu, amma ba a kawo kasafinsu. To abin da ke faruwa a Jihar Ribas ya sa APC ta yi yakinin cewa abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata a kasar nan, don haka akwai bukatar daukar wani mataki akalla domin nuna rashin jin dadin jam’iyyar kan abin da ke faruwa a Najeriya. Kuma ba shakka al’amura sun sauya sakamakon daukar wannan mataki.   
Batun rashin mika kasafin wadannan hukumomin gwamnati ba a zamanin Jonathan aka fara ba, me ya sa sai yanzu za ku dauki mataki?
Ba a zamanin Jonathan aka fara ba, amma wannan bai hana a dauki matakin gyara a yanzu ba. Mu a majalisa in muka ga ba a yin abin da ya dace, muna iya yanke shawarar cewa a yi gyara, kuma shi muka yi kowa kuma yana murna.
Akwai bayanan da ke nuna APC tana fama da rikici a jiharka ta Katsina, kana ganin za ta iya magance wannan rigima har ta lashe zaben badi?
Ina da tabbaci kan za mu lashe zaben 2015 a Katsina. Abin damuwa ne a zaben shekarar 2011 a ce CPC ta kasa lashe zaben Jihar Katsina, muna da yakinin ma ta kafa gwamnati an gama, har ma muna da yakinin CPC za ta kafa gwamnati a matakin kasa da wasu jihohi. To amma siyasa ba haka take ba, a nan Katsina mun samu ’yan jam’iyya marasa kishi da suka yi aiki domin karya jam’iyyar. Amma a wannan karo insha Allahu ba za mu bari haka ta faru ba, domin masu hikima sun ce ba a cizon mutum sau biyu a rami daya. Don haka muna da cikakkiyar fata a wannan karo Katsina za ta kasance ta APC da yardar Allah.
Yaya dangantakarka da jama’ar mazabarka?
Akwai kyakkyawar dangantaka a tsakanina da jama’ata, da za ku je ku nemi ra’ayin jama’a za ku samu amsar cewa akwai kyakkyawar dangataka a tsakanina da su.
Akwai bayanan da ke nuna lokacin rajistar ’ya’yan Jam’iyyar APC, wasu matasa sun kai maka farmaki. Yaya za ka hada wannan da bayaninka na baya?
Kamar yadda na fada cewa da za ku je ku yi kuri’ar jin ra’ayin jama’a za ku fahimci akwai kyakkyawar dangantaka, a yanzu da za ku je haka za ku iske. Domin bayan faruwar wancan hautsini, abin da ya biyo baya shi ne mutane suka rika nuna bacin ransu kan abin da ya faru. Akwai mutanen da suke son kujerata da suka rasa hanyar da za su sa jama’a su yarda za su fi ni yin abin kirki, don haka hanyar da ta saura gare su ita ce su ingiza matasa ko kananan yaran da ba su mallaki hankalinsu ba, su yi min bore, kuma a karshe ba su cimma nasara ba.
Yaya kake ji kan hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabas?
In akwai abin da ya fi damuwa ina yi. Wannan gwamnati ce kullum ke cewa ta gano bakin zaren lamarin, amma har yanzu ta gaza yin komai a kai. Ga fahimtata wannan gwamnati ta gaza, wannan shi ne gaskiyar magana, gwamnatin da ba za ta iya ba, ban san me za a ce kanta ba. Hanyar samun maslaha ita ce a samu gwamnati, to ba mu da gwamnati a fahimtata, lura da abin da ke faruwa a yanzu, domin matsalar tsaro matsala ce mai muhimmanci. A kasashen da suka ci gaba wannan ba zai faru ba, kullum a rika kashe mutane. An ce akwai dokar ta-baci shin dokar ta-bacin tana aiki?
Ka amince da matsayin Gwamnan Jihar Borno ke nan cewa sojojinmu ba su da kayan aiki ko karfin gwiwar yakar ’yan Boko Haram?
kwarai kuwa! A wurina yana da gaskiya, bai kamata a hau shi da surutai ba, domin shi ne abin ke faruwa a gabansa yana gani. Wace nasara aka samu, kullum ana kashe mutane, ko a makon jiya an yayyanka daliban makaranta. Wannan gwamnati ba za ta iya ba, ta gaza. Tabbas Najeriya ta shiga halin yaki, domin idan ba za a iya magance irin wannan yaki na cikin gida ba, wane tabbaci ake da shi, kasar nan za ta iya yakar wata karamar kasa da ka iya kawo mata hari?
Mene ne sirrin da Katsina ke zaune lafiya?
Ban sani ba, wani lokaci abin yakan wuce tunanina. Idan ka lura da yadda lamarin yake, Jihar Borno APC, Yobe APC, Adamawa APC, Katsina PDP. Ban sani ba, dubi Nasarawa inda aka samu rikicin Ombatse, APC, Jihar Ribas APC. Gaskiya abin da ke faruwa a Jihar Borno yana nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta gaza.
 Shin ayyukan da ka gudanar a mazabarka saboda kwadayin komawa kan kujerarka ne ko me ya karfafa maka gwiwar yin haka?
Abubuwa da yawa ne suka karfafa min gwiwa. Na daya babban abin bakin ciki a mazabata duk kananan hukumomin nan uku, ba sa aiki, ba su katabus ko kadan. kananan hukumomi ba su yin komai, hatta a daukacin Jihar Katsina. Kamata ya yi a ce ana samun ci gaba a matakan karkara, amma babu abin da ke gudana, kuma gwamnati ba ta taimakawa a kai.  Wani abin takaici a kwanakin baya an gudanar da gasar kwallo a nan yankin Daura, sai na yanke shawarar in halarci bikin in bayar da kyaututtuka, muka nemi filin wasa amma suka hana mu. Suka hana filin wasan saboda kawai dan Majalisar Tarayya na APC zai kasance a wurin.  Mu a yankin masarautar Daura gwamnatin jiha tana matukar tauye mu, misali a kasafin cike gibi na bara an ware Naira biliyan 10 domin gudanar da ayyukan hanyoyi da raya kasa, amma masarautar Daura ko hanya daya ba a gina ko gyara mata ba kuma ba a yi mata aikin komai daga ciki ba
Muka hakura saboda son zaman lafiya tare da fatar a kasafin bana za a yi abin da ya dace, amma abin takaici ba wani abin kirki da aka shirya yi a yankin masarautar. Abin da kawai aka nuna za a yi shi ne an sanya aikin gyara hanya daya a yankin baure kan Naira miliyan 750. Kuma Kwalejin Nazarin Shari’a ta Yusuf Bala Usman da ke Daura har yanzu gwamnatin jihar ba ta cika ka’idojin da za a amince da kwasa-kwasanta ba. Don haka koda dalibai sun kammala kwas din Diploma a makarantar ba za a dauke su a kowace jami’a ba. Duk ayyukan gwamnatin Katsina ta tare su a yankin Katsina ta Tsakiya.  Wannan ita ce irin gwamnatin da muke da ita a Katsina. To gwamnati ba ta yin abin kirki, kananan hukumomi ba su yin komai, don haka wajibi ne wani ya zo ya yi.
Ba ka ganin asusun hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomi da jihohi ne ya sa kananan hukumomi ba su yin komai, kuma ku a majalisa me kuke yi don magance haka?
Haka ne, wannan shi ne abin da ke faruwa. Kuma in kuna sauraren abin da ke gudana game da gyaran tsarin mulki za ku ji yadda muke kokarin a ba kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu, a soke asusun hadin gwiwa. To amma kun san batun gyara tsarin mulki zai samu nasara ne kawai idan aka samu mafi rinjayen majalisun dokoki na jihohi suka amince da wannan doka. Kuma abin bakin ciki ga Najeriya, galibin ’yan majalisun dokokin jihohin suna aljifan gwamnonin ne. Don haka akwai yiwuwar ba za su amince da wannan doka ba. To amma mu a Majalisar Tarayya mun amince a ba kananan hukumomi ’yancin samun kudadensu kai-tsaye a matsayinsun na zababbun wakilan jama’a.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno