Gwamnatin Katsina za ta bunkasa noman rogo

Shugaban kungiyar manoman rogo ta kasa reshen Jihar Katsina, Alhaji Hassan Yunusa ya ce Jihar Katsina za ta cigaba da bunkasa noman rogo da kuma samar da yanayin sarrafa shi da kuma cinikayyarsa a cikin gida da kuma kasashen ketare. Ya yi wannan bayani ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai  bayan […]

Gwamnatin Katsina za ta bunkasa noman rogo

Shugaban kungiyar manoman rogo ta kasa reshen Jihar Katsina, Alhaji Hassan Yunusa ya ce Jihar Katsina za ta cigaba da bunkasa noman rogo da kuma samar da yanayin sarrafa shi da kuma cinikayyarsa a cikin gida da kuma kasashen ketare.

Ya yi wannan bayani ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai  bayan kammala wata ziyara da shugaban kungiyar na kasa Fasto  Segun Adewumi ya kai jihohin Kano da Katsina, inda kuma ya sanar da cewa Gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari ta na daukar kyawawan matakai na farfado da noman rogo a Jihar ta Katsina da kuma inganta yanayin kasuwarsa.

Ya ce akwai manoman rogo masu tarin yawa a jihar, kuma suna kokarin fadada noman sa ganin cewa noman rogo yana da matukar riba, sannan akwai samar da arziki ga al’umma saboda tarin abubuwan da ake tacewa daga jikinsa na sarrafawa a masana’antu na iki da wajen kasar nan.

Alhaji Hassan ya kuma nunar da cewa za su yi wani tsari wanda zai kawo ci gaba a harkar noman rogo, ta yadda kowane manomi zai amfani noman da yake yi ba tare da wani tsaiko ba, tare da jan hankalin manoman Jihar Katsina da su rika ware wani guri domin sanya rogo wanda a cewarsa ta haka ne za a fadada samar da shi a bira ne da yankunan karkara.

Sannan ya yi godiya ta musamman ga ma’aikatar gona ta jihar da hukumar bunkasa aikin gona da raya karkara ta Jihar Katsina watau KTARDA saboda hada hannu da suke yi wajen kawo canji mai kyau a fannin aikin gona, inda kuma ya jagoranci mahalarta taron zuwa yankin karamar hukumar Batsari don ganin gonakin rogo a bangarori daban-daban.

Daga karshe ya yi amfani da wannan dama, inda ya kara jinjinawa wannan gwamnati ta Aminu Bello Masari saboda kulawa ta musamman da take baiwa fannin aikin gona a fadin Jihar ta Katsina musamman ganin yadda gwamnatin tarayya ta dauki noma a matsayin tsarin farfado da tattalin arzikin wannan kasa, maimakon dawwama da albarkatun man fetur.