Gwamnatin Katsina za ta tallafawa wadanda harin ‘yan bindiga ya raunata

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce gwamnati za ta tallafawa al’ummar da harin ‘yan bindigar da ake zargi da barayin shanu ne da garkuwa da mutane suka kawo harin ramuwar gaiya ta hanyar kone fiye da rabin garin Tsauwa da ke cikin karamar hukumar Batsari da kayan jinkai. Gwamna Masari, ya furta […]

Gwamnatin Katsina za ta tallafawa wadanda harin ‘yan bindiga ya raunata

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce gwamnati za ta tallafawa al’ummar da harin ‘yan bindigar da ake zargi da barayin shanu ne da garkuwa da mutane suka kawo harin ramuwar gaiya ta hanyar kone fiye da rabin garin Tsauwa da ke cikin karamar hukumar Batsari da kayan jinkai.

Gwamna Masari, ya furta hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummomin kauyen Dankar da Tsauwa wadanda suka fuskanci harin ‘yan ta’addar a ranar Jumma’ar da ta gabata.

Daga cikin irin abubuwan da za’a tallafawa al’ummar sun hada da kekunan shanu da na jakai domin saukaka masu wajen neman ruwan da suke fuskantar karancinsa, bayan maharan sun yi awon gaba da nasu gami da kayan abinci.

Har ila yau, zasu samu gudunmawar gyaran hanya daga tsarin bankin duniya. Sannan kuma za’a gina masu makaranta gami da karin jami’an tsaro.

Sai dai Gwamnan ya gargadi al’umma da su guji daukar matakin ramuwar gaiya domin daukar doka ne a hannu. Sannan ya kara tabbatarwa al’ummar Jihar cewa, gwamnatinsa na iya kokarinta na ganin ta samar da tsaro ga al’ummar Jihar.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa