Gwamnatin Kebbi ta biya Naira biliyan 2 na tallafin karatun dalibai
Gwamnatin Jihar Kebbi ta biya kudaden tallafin karatun dalibai da ke fadin jihar. Kwamishinan Ilimi na jihar, Ferfesa Mukhtar Umar Bunza ya ce Gwamnatin Jihar ta biya Naira biliyan biyu, kudaden na tallafin karatu na dalibai ’yan asalin jihar daga shekara ta 2015 zuwa 2018. Kudaden dai sun shafi na rajista da alawus-alawus ga daliban […]

Gwamnatin Jihar Kebbi ta biya kudaden tallafin karatun dalibai da ke fadin jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Ferfesa Mukhtar Umar Bunza ya ce Gwamnatin Jihar ta biya Naira biliyan biyu, kudaden na tallafin karatu na dalibai ’yan asalin jihar daga shekara ta 2015 zuwa 2018. Kudaden dai sun shafi na rajista da alawus-alawus ga daliban jihar da suke karatu a manyan makarantu.
Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Kebbi a kan ci gaban da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya samar a fannin ilimi a jihar. Ya ci gaba da cewa an biya kudin ne domin tabbatar da cewa duk wani dan asalin jihar ya samu ilimi mai zurfi a kyauta.
Kuma ya ce “A shekarar karatu ta 2015/2016, an kashe Naira miliyan 415 da dubu 517 da 800, inda aka biya hukumomin jami’o’i da na kwalejoji sittin na kasar nan kudaden rajistar daliban jihar a wadanan jami’o’i.”
Har ila yau ya ce a shekarar karatu ta 2016/ 2017, an biya Naira miliyan 876 da dubu 717 da 482 ga jami’o’i 21, kuma a shekara karatu ta 2017 /2018, za a biya Naira miliyan 900 da dubu 87 da 529 ga jami’o’i 31 na kasar nan, inda a halin yanzu an gabatar da kasafin kudin a gaban Gwamnan Jihar domin sanya hannu. Saboda haka da zarar an sanya hannu za a biyu kudin ga jami’o’in.
Haka kuma gwamnatin jihar ta horar da malamai da shugabannin da ke kula da hukumomin ilimi a jihar don kara musu ilimi a kan karantarwa ta zamani da kuma yadda tsarin mulki a gefen ilimi yake tafiya a zamanance. Har ila yau ya ce, “Gwamnan Jihar ya ba Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi damar daukar nauyin dalibai dari zuwa kasashen Indiya da China da Turkiya da wasu kasashe domin karatun a wasu fannonin da jihar ke bukata, kamar ilimin aikin jirgin kasa da ilimin hako man fetur da ilimin hako ma’adanai da kuma ilimin fasaha da kere-kere da sauran wasu fannonin.”