Gwamnatin Kebbi ta dora nauyin kulawa da Alhazai ga jami’an da ta nada

Yayin da ake sa ran fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana a ranar Juma’a mai zuwa, Shugaban Kwamitin Aikin Hajjin bana na Jihar Kebbi kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Kanar Sama’ila Yombe Dabai (mai ritaya), ya ce, gwamnatin jihar ta damka maniyyatan a hannun kulawar jami’an da ta nada domin su lura da su yayin aikin […]

Gwamnatin Kebbi ta dora nauyin kulawa da Alhazai ga jami’an da ta nada
Gwamnatin Kebbi ta dora nauyin kulawa da Alhazai ga jami’an da ta nada

Yayin da ake sa ran fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana a ranar Juma’a mai zuwa, Shugaban Kwamitin Aikin Hajjin bana na Jihar Kebbi kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Kanar Sama’ila Yombe Dabai (mai ritaya), ya ce, gwamnatin jihar ta damka maniyyatan a hannun kulawar jami’an da ta nada domin su lura da su yayin aikin Hajjin a kasa Mai tsarki.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya rarraba kwamitocin jami’an da aka nada domin lura da aikin Hajjin bana a Birnin Kebbi.
Shugaban kwamitin ya ce, gwamnati ta zukulo jami’an ne bisa kwarewa da iya aiki da kuma ilimin addini Musulunci da suke da su ganin cewa aikin na addini ne.
Mataimakin Gwamnan ya ce, jami’an sun hada da shi kansa Amirul Hajji da Shugaban Hukumar Gudanarwar Hukumar Alhazai da Sakataren Kwamitin, Alhaji Isah Assalafi da Alhaji Sani Zauro, Shugaban Kwamitin Kula da Sassanin Alhazai da Alhaji Sani Dodo Shugaban Kwamitin Kula da Abincin a filin jirgi da kuma Mohammed Bello Yakubu mai kula da masaukan Alhazai dA Alhaji Bala Giredi mai kula da zirga-zirga da Alhaji Abubakar Umar Babuga watsa labarai da sauransu.