Gwamnatin Kebbi ta taka rawar gani – Ministan Labarai
Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kebbi bisa kokarinta ta tallafa wa kudurin Gwamnatin Tarayya na fidd a kasar nan daga kuncin tattalin arzikin da ta shiga. Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin da ya kai ziyarar aiki na wuni daya inda ya zagaya gonakin wadansu manoma […]

Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kebbi bisa kokarinta ta tallafa wa kudurin Gwamnatin Tarayya na fidd a kasar nan daga kuncin tattalin arzikin da ta shiga.
Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin da ya kai ziyarar aiki na wuni daya inda ya zagaya gonakin wadansu manoma a kananan hukumomin Jega da Aliero da Dandi-Kamba da kuma Suru.
Ministan ya bayyana jin dadinsa game da yadda gwamnatin Jihar Kebbi ke ba da gagarumar gudunmawa wajen tallafa wa Gwamnatin Tarayya wajen fid da kasar nan cikin halin da ta shiga na matsin tattalin arziki a fannin noma.
Lai Mohammed ya ce dalilin zuwansa da ayarinsa Jihar Kebbi shi ne saboda kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafa wa manoma da kuma shaida wa duniya irin kokarin da take yi a fannin noman shinkafa, domin samun karin kamfanoni su shigo domin kafa masana’antun sarrafa shinkafar.
Ya ce, ya zama wajibi a yaba wa gwamnatin Jihar Kebbi a kan yadda take tallafa wa manomanta, domin manoman sun mallaki miliyoyin Naira a karkashinshirin nan na hadin gwiwa tsakanin Babban Bankin Nigeriya (CBN), wato Anco Borrowers da kuma gwamnatin Jihar Kebbi don samar da aikin yi ga matasan kasar nan da kuma rage zaman kashe wando ga marasa aikin yi.
Ministan ya ci gaba da cewa Gwamnatin Tarayya ta fito da wannan shiri ne domin ta farfado da tattalin arzikin da ke cikin noma a kasar nan, musamman bisa la’akari da tabarbarewar tattalin arziki saboda dogaro da danyen man fetur kadai.
A karshe Ministan ya ce, ya zo da ’yan jarida ne domin fada wa duniya irin gagarumar nasarar da aka samu a kan harkar noma, wanda Mai girma Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar a 2015 a Jihar Kebbi.
Shi ma da yake nuna jin dadinsa, Gwamna Atiku Bagudu, ya ce wannan ziyara da Ministan Labarai, Lai Mohammed ya kawo tare da ayarinsa, dama suna jiran irin wannan ta faru, domin kara fada wa duniya irin ci gaban da aka samu a Jihar Kebbi a fannin noma.
Gwamna Bagudu ya ce, baya ga nasarorin da gwamnatin Jihar Kebbi ta samu a fannin noma, ya ce yana son duniya ta sani cewa, suna da wuraren yawon bude ido da suka hada da al’adun Fulani wanda ake ce wa Hurtungo da bikin kamun kifi na kasa da kasa da ake yi a garin Argungu sai kuma bikin al’adar Dakarkari wanda ake kira Uholo wanda ake yi a kasar Zuru da kuma Gande wanda ake yi a kasar Yawuri.
Sai dai Gwamnan ya nuna damuwarsa game da rashin fahimtar juna da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya, yana cewa wannan ba ya da alaka da addini ko kabilanci, inda ya ce matsalar canjin yanayi ne da ya janyo karancin ruwa da filaye, babbar matsalar da ake samu ka kawo rashin fahimta a tsakanin manoma da makiyaya. Sai kuma ya kalubalanci ’yan jaridar da suke cikin ayarin Ministan su tambayi manoma ko makiyaya irin matsalolin da suke fuskantaM su ji daga bakunansu.