Gwamnatin Kebbi za ta aurar da zawarawa 300
Gwamnatin Jihar Kebbi a karo na uku za ta aurar da zawarawa 300 a yinƙurinta na samar da abubuwan dogaro ga mata da kare ƙananan yara da walwalarsu.
Gwamnatin Jihar Kebbi a karo na uku za ta aurar da zawarawa 300 a yinƙurinta na samar da abubuwan dogaro ga mata da kare ƙananan yara da walwalarsu.
Kwamishinan mata da ci-gaban yara, Hajiya Halima Hassan Kamba ta sanar da haka a lokacin da take yi wa manema labarai bayanin ci-gaban da aka samu a ma’aikatarta a birnin Kebbi.
“A watan Yuli na wanan shekara za mu aurar da ma’urata 300 a cikin tsarinmu na auren gata,” cewarta.
Aurar da zawarawa da jihar ke yi ana yin sa da zimmar kawar ayyukan ɓarna da zinace-zinace da kuma ganin an taimaka wa marasa ƙarfi da ke da sana’a amma ba su da ƙarfin yin aure saboda matsalar tattalin arziki.
A cewarta ma’aikatar harkokin mata da ci-gaban yara tana da rawar da za ta taka domin bunƙasa walwala da kare mutuncin mata da ƙananan yara a dukkan jiha.
Kamba ta bayyana gwamnatin su da cewa tana kula da jinsin mata da maza ba tare da samar kowane bambanci ba.
Ta ce gwamnatin ta gyara gidan yara da ke Kawara tare da samar da duk wani abu da yara ke buƙata.
Haka ma gidan gyaran hali na yara na jiha an yi mashi gyara na gaba ɗaya don tabbatar da an ba su kulawa da ta kamata.
Masu sharhi na ganin dacewar dakatar da yin auren Zawarawa zai fi a yankin Arewa a fito da samar da aikin yi da sana’o’in dogaro da kai zai fi dacewa a halin da ake ciki.