Gwamnatin Kebbi za ta yi wa mutum 300 auren gata
Dole a tabbatar cewa kowanne ango na da wata hanyar samun kuɗi ko sana’a ko aikin yi da zai iya ɗaukar nauyin iyalinsa.
Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da shirinta na ɗaukar nauyin auren mutane 300 a karo na uku na shirin auren gata da take gudanarwa.
Shugaban Kwamitin Shirin, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu, ya ce an tantance waɗanda za a yi wa auren gatan daga ƙananan hukumomi 21 da mazaɓu 225 na jihar.
- Manchester United ta ɗauki Youri Tielemans daga Aston Villa
- Kotu ta ɗaure matashi shekara 7 kan mallakar tabar wiwi a Kano
Ya ce gwamnati za ta bai wa kowanne ango naira 250,000 a matsayin sadaki, sannan za ta gudanar da gwajin lafiya ga dukkan ma’auratan kafin ɗaurin aure.
Argungu ya ƙara da cewa an umurci kwamitocin ƙananan hukumomi su tabbatar cewa kowanne ango na da wata hanyar samun kuɗi ta sana’a ko aikin yi da zai iya ɗaukar nauyin iyalinsa.
Ya ce gidauniyar matar gwamnan jihar, NANAS Foundation, za ta samar wa sabbin ma’auratan kayan ɗaki kamar gadaje, katifu da kuma kayan abinci domin sauƙaƙa musu fara rayuwar aure.
Haka kuma, ya ce an kafa kwamitin sa ido da zai riƙa bibiyar rayuwar ma’auratan bayan an ɗaura auren.