Gwamnatin Kogi ta amince da N72,500 a matsayin mafi ƙarancin albashi
Gwamnan ya ce zai ci gaba da aiki don inganta walwalar ma’aikatan jihar.
Gwamnatin Jihar Kogi, ta amince da Naira 72,500 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumomi.
Gwamnan jihar, Usman Ododo ne, ya sanar da hakan bayan karɓar rahoto daga kwamitin mafi ƙarancin albashi a fadar gwamnatin jihar da ke Lokoja a ranar Litinin.
- ’Yan Boko Haram sun fara ɓuya a sansanonin ’yan gudun hijira – Zulum
- Ma’aikatan NAFDAC sun tsunduma yajin aiki
An bai wa kwamitin umarnin yin aiki tare da gano yadda za a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata.
Ododo, ya bayyana cewa za a yi wa ma’aikata a jihar sauye-sauye, sannan ya ƙara da cewa wannan mataki ya cika alƙawarin gwamnatinsa na yi wa al’umma hidima.
Kazalika, ya sanar da dakatar da cire haraji ga dukkanin ma’aikatan gwamnati, na tsawon shekara ɗaya.
“Bayan duba yadda al’amura suke, mun tattauna kuma mun amince da Naira 72,500 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga dukkanin ma’aikata,” in ji Ododo.
Ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su goyi bayan manufar gwamnatinsa na kawo sauyi a jihar.
Shugaban Kwamitin Mafi ƙarancin Albashi kuma shugaban ma’aikata na jihar, Mista Elijah Abenemi, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2024.
Ya ce an kafa kwamitin me don tantance yadda za a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin.
Ya ce kwamitin ya yi jima yana tattaunawa don cimma kyakkyawan sakamako ga ma’aikatan jihar.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) a Jihar Kogi, Kwamared Gabriel Amari, ya nuna godiya ga Gwamna Ododo bisa wannan mataki da ya ɗauka.
Duk da haka, ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da fafutukar neman ƙarin inganta yanayin aiki, ciki har da inganta albashi da alawus na hutu.