Gwamnatin Legas ba ta soke dokar takaita acaba ba

Gwamnatin Jihar Legas ta karyata jita-jitar da ake yadawa, musamman ma a kafofin sadarwa, cewa ta soke dokar da ta yi ta shekarar 2012, wacce ta takaita zirga-zirgar masu sana’ar acaba ko Okada a wasu hanyoyin jihar. A wata takardar sanarwar da gwamnati ta sanyawa hannu, ta ce ba ta da niyyar soke dokar, saboda […]

Gwamnatin Legas ba ta soke dokar takaita acaba ba
Gwamnatin Legas ba ta soke dokar takaita acaba ba

Gwamnatin Jihar Legas ta karyata jita-jitar da ake yadawa, musamman ma a kafofin sadarwa, cewa ta soke dokar da ta yi ta shekarar 2012, wacce ta takaita zirga-zirgar masu sana’ar acaba ko Okada a wasu hanyoyin jihar. A wata takardar sanarwar da gwamnati ta sanyawa hannu, ta ce ba ta da niyyar soke dokar, saboda ta yi ta ne sakamakon kiraye-kirayen da jama’a suka rika yi kan ta dauki mataki a kan sana’ar okada a jihar. Takardar sanarwar, wacce mai taikama wa Gwamna kan harkokin yada labarai, Mista Lateef Raji ya sanya wa hannu, ta nuna cewa gwamnati ba ta da niyyar ta mayar da kanta baya a kan batun okada a jihar. Mista Raji ya kara da cewa matakin da gwamnati ta dauka kan sana’ar okada ta haifar da samun nasara wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar. Ya ce dokar da gwamnati ta yi kan sana’ar Okada ba hana sana’ar ta yi kwata-kwata ba, sai dai ta takaita zirga-zirgar masu sana’ar ne ga wasu hanyoyin jihar, wanda hakan ya haifar da nasarori masu yawa. Sanarwar ta bayyana cewa a lokacin da masu sana’ar ke yinta barkatai babu tsari ana samun asarar rayuka 16 tare da samun ranuka 646 a duk wata, amma da aka fara aiwatar da dokar, yawan mutanen da ke mutuwa ya ragu zuwa biyu, masu raunuka kuma 100 a duk wata. Ya bukaci masu sana’ar okada su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda doka ta tanada a jihar ta Legas. Jita-jitar cewa gwamnatin jihar ta janye dokar hana sana’ar acaba a jihar ta rika yaduwa, kamar wutar daji, inda  masu sana’ar suka rika gudanar da harkokinsu a hanyoyin da gwamnati ta hana. Aminiya ta gano cewa wadanda suka daina sana’ar sun koma sana’ar ba tare da wani jinkiri ba. Masu sana’ar okada a jihar sun bayyana rashin jin dadinsu da jin sanarwar da gwamnati ta fitar, wacce ta karyata jita-jitar da suka ji.