Gwamnatin Legas da kungiyar AYF sun yi wa cutar maleriya taron dangi
Gwamnatin Jihar Legas da hadin gwiwar kungiyar kare ’yancin ’yan Arewa mazauna Legas (AYF) sun gudanar da bikin yakin da cutar maleriya don wayar da kan al’umma kan illar cutar a jihar.An yi bikin ne a harabar filin wasa na barikin sojoji da ke Marine Beach a yankin Apapa a karshen makon da ya gabata. […]

Gwamnatin Jihar Legas da hadin gwiwar kungiyar kare ’yancin ’yan Arewa mazauna Legas (AYF) sun gudanar da bikin yakin da cutar maleriya don wayar da kan al’umma kan illar cutar a jihar.
An yi bikin ne a harabar filin wasa na barikin sojoji da ke Marine Beach a yankin Apapa a karshen makon da ya gabata. Da yake jawabi, shugaban karamar Hukumar Apapa, Honarabil Ayodeji Joseph ya jaddada kudurin karamar hukumar wajen ci gaba da yaki da cutar maleriya a yankinsa. Mista Ayodeji ya bayyana cewa kara-mar hukumarsa a shirye take don ba da gudunmawa ga sashen lafiya na jihar don cimma burin da aka sa a gaba.
A jawabinsa, shugaban kungiyar kare ’yancin Arewa ta AYF, Alhaji Umar A. Yaro ya bayyana cewa kungiyarsa ta shirya taron ne don ilimantar da jama’a kan illar cutar maleriya.
Ya bayyana cewa kungiyar AYF za ta ci gaba da shirya taruka kan sha’anin kiwon lafiya don fadakar da jama’a illolin da ke tattare da cututtuka daban-daban.
A wurin taron Kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Jide Idris ya yaba wa kungiyar AYF saboda kokarin da take yi na ilimantar da jama’a da fadakar da su kan cutar maleriya da sauran cututtuka masu kisa.
Ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar lafiya ta jihar za ta ci gaba da aiki tare da kungiyar AYF don cimma burin da aka sa a gaba a bangaren kiwon lafiya a jihar.
A wurin taron an raba kyautar gidan sauro da maganin kashe kwari da ba da magani da awon jini ga masu fama da cutar ta maleriya da hawan jini da ciwon suga da cutar kanjamau. Sarakunan Hausawan Jihar Legas da manyan jami’an gwamnati daga ma’aikatar lafiya ta jiha da karamar Hukumar Apapa sun halarci taron.
Daga bisani an gudanar da wasan kwaikwayo cikin harshen Hausa kan yadda jama’a za su kare kansu daga kamuwa da cutar maleriya.