Gwamnatin Legas ta amince da sanya Hijab a makarantu
Gwamnatin jihar Legas ta amince da sanya Hijab ga dalibai mata musulmi a makarantun Gwamnatin. An sanar da hakan ga duk reshen kungiyoyin dalibai musulmi (MSSN) ta Najeriya. A watan Oktoba na 2014 babbar kotun jihar Legas ta yi watsi da batun sanya hijabi a makarantun, yayin da kotun daukaka kara ta nemi a sake […]
Gwamnatin jihar Legas ta amince da sanya Hijab ga dalibai mata musulmi a makarantun Gwamnatin.
An sanar da hakan ga duk reshen kungiyoyin dalibai musulmi (MSSN) ta Najeriya.
A watan Oktoba na 2014 babbar kotun jihar Legas ta yi watsi da batun sanya hijabi a makarantun, yayin da kotun daukaka kara ta nemi a sake sauya batun sanya hijab din a watan Yuli 2016.