Gwamnatin Legas ta hana mata shigar banza

Gwamnatin Jihar Legas ta hana mata ma’aikata sanya kaya masu nuna tsaraici a gine-gine da ma’aikatun jihar.Gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yawan sanya kaya masu nuna tsaraici da ma’aikata mata suke yi a Sakatariyar Gwamnatin Jihar da ke Alausa.Binciken Aminiya ya gano cewa mata ma’aikata na sanya kaya masu nuna tsaraici ne a lokacin […]

Gwamnatin Legas ta hana mata shigar banza

Gwamnatin Jihar Legas ta hana mata ma’aikata sanya kaya masu nuna tsaraici a gine-gine da ma’aikatun jihar.
Gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yawan sanya kaya masu nuna tsaraici da ma’aikata mata suke yi a Sakatariyar Gwamnatin Jihar da ke Alausa.
Binciken Aminiya ya gano cewa mata ma’aikata na sanya kaya masu nuna tsaraici ne a lokacin da za su shiga cikin sakatariyar gwamnatin jihar. Kuma gwamnatin jihar ta ce yawaitar lamarin da yadda wasu suke wuce gona da iri ne ya tilasta gwamnatin bullo da tsarin haramta sanya kaya.
Takardar umarnin ta fito ne daga ofishin shugaban ma’aikatan jihar Misis Josephine Williams tun ranar 7 ga Fabrairun nan kuma tuni aka tura wa ma’aikatun.
Takardar ta umarci daraktocin kudi da mulki su tabbatar da daukan matakin ladabtarwa ga duk ma’aikaciyar da aka samu da karya dokar. Takardar mai lamba: CIR/HOS/14/bOL.1/022, ta ce an ba da irin wannan umarnin a shekarar 2005 a takarda mai lamba: 113 wacce ta umarci duk wani ma’aikaci ya rika sanya kayan da suka dace a wurin aiki da lokacin da ya fita aiki.
Takardar ta ce sanya kayan da suka dace na nuna kyawawan shirye-shirye da manufofin gwamnatin jihar.
Shugabar Ma’aikatan Jihar, Misis Josphine Williams ta ce duk siket din da bai kai kwauri ba, ya saba wa doka saboda haka ma’aikata kada su sanya shi. Kuma ta ce duk kayan da ya matse jiki ko kuma duk kayan da zai nuna tsaraici, ba a yarda ma’aikaciya ta sanya su ba.
Ta ci gaba da cewa idan ya zama dole sai ma’aikciya ta sanya siket ko wando, to ya zama bai dame ta ba kuma ba ya nuna tsaraici kuma dole a sanya shi tare da riga jaket.
Rigunan da ake so a sanya a cewarta sun hada da rigar da ta kai kwauri wacce ba ta dame jiki ko nuna tsaraici. Ta ce idan za a sanya kayan gargajiya to dole a sanya su cikakku, kuma kayan da aka sahale wa maza su sanya har da kwat da madaurin wuya.