Gwamnatin Legas ta kwace sama da motoci 100 da suke kwana a kan gadoji

Gwamnatin ta ce za ta kai dukkansu kotu don hukunta su

Gwamnatin Legas ta kwace sama da motoci 100 da suke kwana a kan gadoji

Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta ce ta kwace motoci sama da 100 da ake ajiye su a kan gadoji.

Motocin da aka kama sun hada da na haya da ma wadanda ba na haya ba.

An yi kamen ne a karshen wa’adin mako daya da gwamnatin Jihar ta ba masu motocin bas-bas da tifofi da ta ce sun mayar da kan gadojin a matsayin wuraren ajiye motoci da na gyaransu.

Mai ba Gwamnan Jihar shawara kan harkokin sufuri, Sola Giwa ne ya jagoranci aikin duba ababen hawan.

Ya ce sun dauki matakin ne domin tsaftace hanyoyi da kawo karshen yadda ababen hawa suke kawo cunkoso a kan gadojin.

Sola ya ce an kwace ababen hawan ne a kan gadojin da ke unguwannin Ejalonibu da Obalende da Apongbon Ebute-Ero, Idumota da ke Jihar.

Hadimin Gwamnan ya ce za su ci gaba da aikin har sai sun tsaftace hanyoyin jihar daga cunkoso kamar yadda gwamnatin Jihar mai ci ta kuduri aniyar yin haka.

Sai dai ya ce nan ba da jimawa ba za su gurfanar da dukkan motocin a gaban kotun tafi-da-gidanka ta ababen hawa domin su fuskanci hukunci.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba