Gwamnatin Legas ta rarraba kayan ofis ga kungiyoyin makarantun gaba da sakandare 10

Gwamnatin Jihar  Legas ta  rarraba  kayayyakin aikin  ofis  ga kungiyoyin dalibai  na makarantun gaba da sakandare 10 da ke jihar, domin inganta harkokin ofisoshin kungiyoyin nasu. Makarantun su ne Jami’ar Jihar Legas da Kwalejin Ilimi ta Adeniran Ogunsanya da Kwalejin Ilimi ta Yaba da Kwalejin Ilimin Teku (Oceanography) ta Gwamnatin Tarayya da Kwalejin Gwamnatin Tarayya […]

Gwamnatin Legas ta rarraba kayan ofis ga kungiyoyin makarantun gaba da sakandare 10
Gwamnatin Legas ta rarraba kayan ofis ga kungiyoyin makarantun gaba da sakandare 10

Gwamnatin Jihar  Legas ta  rarraba  kayayyakin aikin  ofis  ga kungiyoyin dalibai  na makarantun gaba da sakandare 10 da ke jihar, domin inganta harkokin ofisoshin kungiyoyin nasu. Makarantun su ne Jami’ar Jihar Legas da Kwalejin Ilimi ta Adeniran Ogunsanya da Kwalejin Ilimi ta Yaba da Kwalejin Ilimin Teku (Oceanography) ta Gwamnatin Tarayya da Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Fasaha da Kwalejin Ilimin Firamare ta Micheal Otedola da kuma Kwalejin Ilimi ta St. Augustine; sai  kuma Kwalejin Fasahar Lafiya ta Jihar Legas.
Kayayyakin da  aka  rarraba  wa  kungiyoyin  daliban sun  hada  da  komfutoci da injinan gurza  takardu da kujerun ofis da na’urar sanyaya daki da kuma  firjin. A bikin bayar da kayayyakin, kwamishinar ilmi  ta jihar,  Misis Olayinka Oladunjaye ta shawarci daliban su yi amfani da kayayyakin ta hanyar da ta dace, kuma su dauka tamkar kayansu ne da  suka saya da kudinsu.
Ta ce gwamnati ta yi hakan ne domin daliban su samu  damar tafiyar da harkokin mulkin kungiyoyinsu cikin sauki kuma ya agaza musu wajen harkokin karatunsu.  Saboda haka ta bukaci kada su dauka wata toshiyar baki ce kan  al’amurran gwamnati.
Da yake tofa  albarkacin bakinsa, Mai baiwa  gwamna shawara  a hakokin ilimi, Otunba Fatai Olukoga ya ce  duk da yake kayayyakin an baiwa  shugabannin kungiyoyin daliban ne, sauran daliban na da  damar  cin gajiyarsu, illa  kawai  shugabannin su tabbatar ba a lalata  su  ba.
Da yake jawabin godiya, shugaban dalibai na makarantun gaba da sakandare na jihar, Mista Eleto Yakubu ya ce su kadai suka san irin wahalar da suke sha  wajen tafiyar  da  harkokin mulkin kungiyoyinsu, musamman a yayin suke son aikewa da sakonni.
Haka nan ya yaba wa gwamnatin jihar kan wasu  gine-gine da take yi a wasu  makarantun nasu  wadanda suke taimaka wa  harkokin karatu.
Daga karshe ya yi fatan sauran gwamnatoci  za su  rika yi wa  dalibai  irin wannan taimakon da zai inganta  iilmi  sannan  zai kara  dankon zumunta  tsakanin gwamnatoci  da kungiyoyin dalibai.