Gwamnatin Legas ta rufe mujami’u da masallatai
Gwamnatin Jihar Legas ta rufe akalla mujami’u 53 da masallatai da otel-otel a sassa daban-daban na jihar bisa dalilan karar amsakuwar da suke cutar da makwabtansu.Babban Manajan Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar, Adeola Shabi ya ce mutanen da ke makwabtaka da wuraren da hukumar ta rufe ne suka yi ta korafin cewa wuraren bautar […]
Gwamnatin Jihar Legas ta rufe akalla mujami’u 53 da masallatai da otel-otel a sassa daban-daban na jihar bisa dalilan karar amsakuwar da suke cutar da makwabtansu.
Babban Manajan Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar, Adeola Shabi ya ce mutanen da ke makwabtaka da wuraren da hukumar ta rufe ne suka yi ta korafin cewa wuraren bautar da otel-otel din suna uzzura musu da hayaniya ta amsakuwa, wanda hakan ya sanya hukumar ta rufe su, bayan da ta yi mauu gargadin rage sautin da suke amfani da shi amma suka yi kunnen uwar shegu.
Ya kara da cewa mafiya yawan wuraren bautar, asalinsu gidaje ne na zama aka mayar da su wuraren bauta, wanda hakan ne ya sanya su kuntata wa masu makwabtaka da su kuma hukumar ta sanar da su adadin karfin sautin da ya kamata su yi amfani da shi da rana da wanda ya dace a sanya cikin dare amma suka yi kememe, wanda hakan ya sa ta rufe su.
Wannan mataki na hukumar ya zo a kan gaba, domin a yanzu mafiya yawan gidajen haya a Legas da Abeokuta za ka ga ana ware wasu bangare ana gudanar da majami’a. Kamar yadda wani da aka sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu: “Ni ma hakan ya faru da ni, da na nemi gida zan kama haya sai mai gidan ta fada min cewa a duk mako akwai ranar da ake kwana ana yin bauta a majami’a a saman benen gidan, wanda hakan ya sanya na hakura da gidan; kodayake har yanzu ba a rabu da Bukar ba, domin a lokuta da dama kade-kade da raya-rayen majami’un da ke makwabtaka da mu kan hana mu runtsawa a cikin dare,” inji shi.