Gwamnatin Legas ta sake kulle Kasuwar Ilepo saboda ƙazanta
Wata 10 da suka gabata, an rufe kasuwar na kusan mako huɗu saboda tarin ƙazanta.
A karo na biyu cikin shekara ɗaya gwamnatin Legas ta sake kulle Kasuwar Kayan Abinci ta Ilepo, a ranar Lahadin da ta gabata saboda dalilan da ta bayar na rashin tsafta a kasuwar.
Kasuwar Ilepo ita ce kasuwar kayan abinci mafi girma a Jihar Legas bayan Kasuwar Mil 12.
- ‘Dalilin da ba a samun isasshiyar wutar lantarki a Nijeriya’
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a iyakar Nijar da Najeriya
Jami’an Hukumar Kula da Shara ta Jihar Legas (LAWMA) ne suka rufe kasuwar a yammacin Lahadin da ta gabata.
Aminiya ta tuntuɓi ɗaya daga cikin shugabannin kasuwar Alhaji Ɗan Galadima wanda ya ce yana Arewa tun da mutane suka yi awon gaba da Sallah kuma ba ya da masaniya kan haka.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin wasu shugabannin amma lamarin ya ci tura, sakamakon kasancewar kasuwar a rufe.
Wata 10 da suka gabata, an rufe kasuwar na kusan mako huɗu saboda rashin tsabta da tarin ƙazanta.
An jibge manyan motocin kwashe shara na Hukumar LAWMA a kasuwar yayin da aka garƙame ta, aka hana sauke kaya da akasarinsu ke zuwa daga Arewa, aka kuma hana masu shiga kasuwar su saya, waɗanda yawancinsu ’yan sari ne.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Legas ba ta ce uffan kan rufe kasuwar ba.