Gwamnatin Legas ta taimaka wa hukumar NDLEA da motoci
Gwamnatin Jihar Legas ta ba da gudunmowar motoci kirar a-kori-kura ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin ta kara azama ga aikin ta na fatattakar masu wannan mummunar sana’ar ciki da wajen Najeriya.Da yake mika motocin ga shugaban hukumar na kasa, Gwamna Babatunde Fashola ya ce gwamnatin ta yi […]

Gwamnatin Jihar Legas ta ba da gudunmowar motoci kirar a-kori-kura ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin ta kara azama ga aikin ta na fatattakar masu wannan mummunar sana’ar ciki da wajen Najeriya.
Da yake mika motocin ga shugaban hukumar na kasa, Gwamna Babatunde Fashola ya ce gwamnatin ta yi haka ne domin ta kara wa hukumar kwarin gwiwar gudanar da ayyukanta, musamman ganin jihar na da manyan tashoshin sufuri na duniya daban-daban.
Gwamnan ya nemi gwamnatin tarayya da kuma musamman majalisun kasa su samar da hukunci mai tsanani ga masu safara da shan miyagun kwayoyi, domin hukuncin da ake yanke musu ya sa da yawansu bayan an yi musu hukuncin, sai su sake komawa ruwa. “kasashen da suke da hukunci mai tsanani, wanda wasu har kashewa ake yi, lamarin ya takaita, saboda haka idan ba a tsananta hukunci ba, to duk wani kokari da hukumar take yi zai zama ragagge”. Inji shi.
Da yake karbar motocin, shugaban hukumar, Alhaji Amadu Giade cewa ya yi kalubalen da hukumar ke fuskanta a jihar ya sha bamban da na sauran jihohin, musamman da yake jihar tana da yawan jama’a, wanda karade kowane lungu shi kansa wani babban aiki ne duk da hukumar tana da ofisoshi a sassan jihar daban-daban.
Alhaji Giade ya ce bincike ya nuna akwai wani abu na musammam da jihar ke da shi wanda babu a sauran jihohin, lamarin da ya sa masu fatauci suka fi mayar da hankalinsu a jihar, kodayake kame wasu gidajen da ake sarrafa hodar ‘mitapitamin’ wadda ta fi hodar koken illa ya sa sun sake wani matsugunni, wanda ko’ina suka shiga cikin Najeriya za a zakulo su.
Ya ce wadannan motoci da gwamnati ta baiwa hukumar, za su kara mata kwarin gwiwar gudanar da ayyukanta.
Alhaji Giade ya ce tsarkake kasa daga mummunan dabi’u nauyi ne da ke kan duk wani dan kasa nagari, don haka sauran jama’ar kasa na iya sa baki wajen ganin an kara tsananta hukuncin da ake da shi yanzu kan masu fataucin.