Gwamnatin Legas ta yi watsi da mu -sarkin kabilar Ijaw na Legas
Shugaban majalisar sarakunan Ijaw kuma sarkin kabilar Ijaw na Jihar Legas, Cif Aled Sikaboro JP ya ce gwamnatin jihar ta Legas ba ta damawa da su a al’amuran gudanarwar jihar. Cif Aled ya yi furucin haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Legas a makon da ya gabata, inda ya yi nunin cewa, […]

Shugaban majalisar sarakunan Ijaw kuma sarkin kabilar Ijaw na Jihar Legas, Cif Aled Sikaboro JP ya ce gwamnatin jihar ta Legas ba ta damawa da su a al’amuran gudanarwar jihar.
Cif Aled ya yi furucin haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Legas a makon da ya gabata, inda ya yi nunin cewa, “Gwamnatin ba sa ba mu sarautar gargajiya kuma ba su dauki sarautunmu da muhimmanci ba. Gwamnatin Legas ta yi watsi da mu, ta yadda hatta mukaman siyasa ba sa ba mu. Su yadda tsarinsu yake a nan Legas ba sa damuwa da sarauntun gargajiya na baki”.
Ya ci gaba da cewa, “Saboda haka nake so na yi amfani da wannan dama na yi kira ga jama’armu su rika shiga siyasa ko za a rika ba su mukaman siyasa a jihar”.
Ya bayya cewa babban kalubalen da ke fuskantar su shi ne yadda gwamnatin Legas za ta san da zamansu a jihar. Ya kuma yi nunin cewa kan al’ummar Ijaw mazauna Legas a hade yake, musamman domin ba wanda ya taba fitowa yana rikici da shi a kan sarauta. Ya ce, “Ka ga wannan ya isa ya nuna maka cewa muna da hadin kai tamkar tsintsiya madaurinki daya. Haka lamarin yake game da kungiyar kabilar Ijaw ta INC, wadanda su ma kansu a hade yake ba wani bambanci”.
A karshe Cif Aled ya nuna takaicinsa dangane da rashin ganin shugaban kasa duk lokacin da ya kawo ziyara Jihar Legas. “Abin takaici ne, sai shugaban kasa ya zo Legas, amma ba ma sani. Da ya zo, idan ya gama abin da ya kawo shi, sai ya koma”. Inji shi.