Gwamnatin Legas za ta raba wa dalibai katin cirar kudi na ATM

Gwamnatin Jihar Legas za ta raba wa daliban manyan makarantu katin ciro kudi daga na’urar ATM, wannan kuwa yunkuri ne na talalfa wa wadanda suka samu gurbin karo ilimi a makarantun gaba da sakandare, don haka za a ware wasu bankuna da za a rika raba wa daliban tallafi, a cewar gwamantin.Gwamnatin, ta ce, maimakon […]

Gwamnatin Legas za ta raba wa dalibai katin cirar kudi na ATM
Gwamnatin Legas za ta raba wa dalibai katin cirar kudi na ATM

Gwamnatin Jihar Legas za ta raba wa daliban manyan makarantu katin ciro kudi daga na’urar ATM, wannan kuwa yunkuri ne na talalfa wa wadanda suka samu gurbin karo ilimi a makarantun gaba da sakandare, don haka za a ware wasu bankuna da za a rika raba wa daliban tallafi, a cewar gwamantin.
Gwamnatin, ta ce, maimakon ta rika bin su makarantun nasu tana ba su kudi abu mai sauki ne, ta rarraba musu katun an wasu bankuna, wadanda za a biya kudin a cikinsu, iyaka dai samu alamar cewa kudi ya shiga asusun ajiyar su, inda su kuma za su cire a duk lokacin da bukata ta taso.
Shugabar hukumar kula da Jin dadin dalibai ta jihar, Madam Omoutun Yetunde Jegede, ta ce, ba dole ne daliban su karbi wannan kati a rana guda ba, kowa na iya zuwa ranar da yake so, amma daga karfe takwas zuwa uku na kowace rana. Kuma dalibi ya tabbatar sunan sa na cikin jerin wadanda aka bai wa alawus din.
Ta ce, abin da ke bai wa dalibi damar samun kudin sun hada da takardar shaidar samun gurbin karatu a makarantar da ke wuri kaza, tare da sakamakon jarabawar da ya bayar damar samun wannan makarantar, da kuma takardar shaidar biyan haraji, na babanka ko kuma wani mai daukar dawainiyar karatun ka.
Sannan ta ce, ba da wannan alawus din bai takaita ga wasu kwasa-kwasai ba, sai dai ba kudi guda ake bai wa kowa ba, ya danganta ga irin kwas din da mutum ke yi.