Gwamnatin Libya ce ta hana Super Eagles sauka a Benghazi —Matukin Jirgi

Matukin jirgin da ya kai tawagar Super Eagles kasar Libya, ya ce manyan hukumomin kasar Libya ne suka bayar da umarnin karkatar da jirgin zuwa Al-Abraq

Gwamnatin Libya ce ta hana Super Eagles sauka a Benghazi —Matukin Jirgi

Matukin jirgin da ya kai tawagar kwallon kafar Najeriya, Super Eagles kasar Libya, ya ce manyan hukumomin kasar Libya ne suka bayar da umarnin karkatar da jirgin zuwa wani filin jirgin sama mai nisa, Al-Abraq daga Benghazi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayani kan dalilin karkatar da akalar jirgin nasu ba zato ba tsammani zuwa Al-Abraq, maimakon inda suka nufa wato Benghazi.

A cikin wani bidiyo da dar jaridar wasanni Pooja Media ta wallafa a ranar Talata, matukin jirgin ya jaddada cewa ba da shi da kansa ya yanke hukuncin ba, manyan hukumomin Libya ne suka ba da umarni.

Matukin jirgin na Super Eagles ya ce ya sha kalubalantar umarnin karkatar da jirgin Super Eagles saboda “A harkar sufurin jiragen sama muna da tsari, muna lissafin man fetur zuwa inda za mu, don haka dole ne mu kauce wa irin wannan abu domin yana iya haddasa matsala.

“Lokacin da na nemi sauka a Benghazi bisa tsarin da aka yi na farko da kuma izinin da na samu, sai suka ce a’a. Da na ba zai yiwa ba, sai suka ce umarni ne daga sama, saboda haka ne ku sauka a Al-Abraq.”

Ya kara da cewa “An tsara cewa jirgin za sauka ne a Benghazi, Benina, kuma mun samu izinin yin hakan daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Libya.

“Amma da muka fara kokarin saukowa, sai suka umarce mu da mu juya akalar jirgin mu je mu sauka a Al-Abraq, mai tazarar kusan kilomita 300.

“Al Baraq ba ya ma cikin jerin filin jirgin sama da aka tsara cewa za mu iya sauka idan akwai wani abu, wanda hakan ba abu mai kyau ba ne,” in ji shi.

Matukin jirgin ya bayyana karkatarwar a matsayin mai hatsarin gaske, yana mai nuni da yawan man da aka yi lissafin jirgin zai sha yayin fara tafiyar.

Tun a ranar Lahadin ake cece-kuce kan tun bayan tawagar Najeriyar da ke kan hanyarta ta zuwa birnin Benghazi domin taka leda a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ta yi da Libya a ranar Talata 2025.

Bayan karkatar da jirgin zuwa Al Baraq, tawagar ta shafe sama da sa’o’i 16 ba tare da samun abinci ko masauki ko damar barin filin jirgin ko motocin sufuri zuwa Benghazi ba.

Al Abraq karamin filin jirgin sama ne da aka kebe don ayyukan jigilar masu zuwa aikin Hajji.

Rikicin PDP: Gwamnoni sun ba Damagum wa’adin yin murabus

DAGA LARABA: Me Ya Sa Kimar Dattawa Ta Ragu A Cikin Al’umma?

Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili