Gwamnatin Masar ta karbe iko da masallatan kasar
Hukumomin kasar Masar sun yanke shawarar karbe iko da masallatai masu zaman kansu a cikin kasar, a wani mataki na sa ido a kan masu kishin Musulunci.Ministan Kula da Harkokin Addini na kasar Mohammed Mokhtar ya umarci jami’an ma’aikatarsa cewa nan da wata guda su karbe iko da masallatan.Akwai masallatai fiye da dubu 130 a […]
Hukumomin kasar Masar sun yanke shawarar karbe iko da masallatai masu zaman kansu a cikin kasar, a wani mataki na sa ido a kan masu kishin Musulunci.
Ministan Kula da Harkokin Addini na kasar Mohammed Mokhtar ya umarci jami’an ma’aikatarsa cewa nan da wata guda su karbe iko da masallatan.
Akwai masallatai fiye da dubu 130 a kasar Masar kuma kusan masallatai dubu 10 daga cikinsu dama suna karkashin ikon gwamnatin kasar ne, yayin da sauran suke karkashin kungiyoyin daban-daban.
A cikin watan Junairun da ya gabata gwamnatin Masar ta fito da tsarin takaita ikon masallatan kasar na yin huduba a kashin kansu, inda ta ce ita za ta rika ba masallatan irin hudubobin Sallar Juma’a da za su rika gabatarwa, duk dai a wani yunkuri na dakile tasirin masu kishin addinin Musulunci.
Kafin nan, gwamnatin ta kori dubban masu wa’azin Musulunci, bisa hujjar ba su cancanci gudanar da wa’azi ba.
Tunda masu ra’ayin raba addini da siyasa suka hada kai da sojojin Masar aka kawar da gwamnatin magoya bayan kungiyar Ikhwanul Muslimina ta kasar Masar a karkashin shugabancin Mohammed Mursi a watan Yulin bara, gwamnatin kasar take ta bullo da hanyoyin dakile masu kishin addini a kasar, inda ta haramta ayyukan kungiyar Ikhwanu da kuma kungiyar Hamas ta kasar Falasdinu a makon jiya.