Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin shari’a kan Binance

Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga hannun mahukunta a Abuja.

Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin shari’a kan Binance

Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙara kan kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Hukumar Tara Haraji ta Kasa, FIRS ce ta sanar da matakin a cikin ƙarar da shigar mai lamba FHC/ABJ/CR/115/2024.

Gwamnatin dai na tuhumar kamfanin na Binance da aikata laifuka huɗu da ke da alaƙa da ƙin biyan haraji.

Cikin waɗanda ake ƙarar akwai Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, dukkansu manyan shugabannin Binance da yanzu haka ke tsare a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Binance sun haɗa da zargin ƙin biyan harajin VAT kan kayayyakin more rayuwa da harajin da kamfanoni ke biya na kuɗin shigar da suke samu da ƙin biyan kuɗaɗen harajin da suka karɓa da kuma haɗa baki da abokanan hulɗarsu wajen kaucewa biyan haraji ta shafinta.

A cewar gidan Talabijin na Channels, Gwamnatin Najeriya tana zargin Binance da ƙin yin rajista da Hukumar FIRS saboda dalilai na haraji da kuma saɓawa dokokin biyan haraji a ƙasar.

Ɗaya daga cikin tuhumar da ake yi ta shafi gazawar Binance na karɓa da kuma biyan nau’o’in haraji ga gwamnati kamar yadda yake a sashe na 40 na dokar FIRS ta 2007 da aka yi wa gyaran fuska.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan ƙudurinta na tabbatar da cewa kamfanonin kirifto suna mutunta dokokinta na haraji tare da magance almundahana a tsakanin irin kamfanonin.

Sai dai a bayan nan ne Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, ɗaya daga cikin jiga-jigan na Binance da ke tsare, Nadeem Anjarwalla, ya tsere daga hannun mahukunta a Abuja.

Jaridar ta ruwaito cewa, Mista Anjarwalla wanda ya yi amfani da fasfo ɗin ƙasar Kenya ya tsere ne bayan ya sulale daga hannun waɗanda ke tsaronsa a yayin da suka yi rakiyarsa wani masallaci domin yi sallah a babban birnin ƙasar.

HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS