Gwamnatin Najeriya ta ciyo bashin N11trn a wata guda

Bashin da ake bin kasar ya karu zuwa Naira tiriliyan 31.15 daga tiriliyan 19.83

Gwamnatin Najeriya ta ciyo bashin N11trn a wata guda

Gwamnatin Najeriya ta ciyo karin bashin Naira tiriliyan 11.33 a watan Agustan 2024.

Hakan ya kara yawan bashin da ake bin kasar zuwa Naira tiriliyan 31.15 daga Naira tiriliyan 19.83 da ake bin ta a watan Yuli.

An biyo kowane dan kasar mai yawan al’umma miliyan 220 bashi na Naira 51,500 a watan Agustan 2024, jimillar bashin da ake bin sa kuma N141,590.

Alkaluman kudi da lamuni na Babban Bankin Najeriya (CBN) sun nuna cewa a cikin wata daya kacal kasar ta karbo fiye da kashi 57.1 cikin 100 na bashin da ake bin ta.

Bayanan sun nuna cewa kai kashi 29.4% na Naira tiriliyan 105.88 a da ake bin kasar a watan Agusta, basuka ne na cikin gida.

Hakan na zuwa ne saboda gwamnati na ci gaba da dogaro da lamuni na cikin gida don gugdanar da harkokinta.

Yawan rancen da gwamnati ke karba ya nuna yadda hannun jarin gwamnati ke kara daraja, sakamakon karuwar yawan ribar da ake samu saoda kara kudin ruwa da CBN ke ci gaba da yi.

Yawan kudin ruwan yana sa kadarorin gwamnati su zama abin sha’awa ga masu zuba jari.

Sai dai duk da haka kamfanoni masu zaman kansu sun dan samu raguwar lamuni yayin da suka dage wajen biyan basussuka sakamakon tasirin hauhawar farashin ruwa, wanda ya sa rancen kuɗi ya fi tsada ga ’yan kasuwa yayin da yake kara wa asusun gwamnati farin jini.

Zuwa watan Agustamn 2023 jimillar bashin da gwamnati ta karba Naira tirilitanN22.51 ne.

Hakanna nufin a shekara guda cin basin ya karu da kashi 38.5%, wanda ke kara tabbatar da dogaron gwamnati a kan bashi wajen gudanar da ayyukanta.

Kamfanoni na gudun bashi

A yayin da gwamnati ke kara cin bashi, kamfanoni masu zmaan kansu kuma ja da baya suke daga karba.

A watan Agustan 2024, bashin da ake bin kamfanoni masu zaman kansu Naira triiliyan N74.73 ne, wanda karin da aka ba shi da yawa a kan tiriliyan N75.51 da ake bin su a watan yulin.

Wannan ragin na nuni da yadda kamfanoni ke wahala wajen viyan basukan da suka karba, a sakamakon karin kudin ruwa da bankin CBN ya yi.

A watan Agustan 2023 bashin da ake bin su Naira tiriliyan N56.95 ne, wanda halin da ake cikin a yanzu ke nuni da cewa a shekara guda da ta gabata an samu karubar karbar bashi a bangern, amma yawan bashin na kawo musu cikas, shi ya sa suka dakata.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025