Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki

Batun karin na zuwa ne bayan a bara gwamnatin ta yi ninka kudin wuta sau uku ga kwastomomi da ke amfani da Band A.

Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirye-shiryenta na sake kara kudin wutar lantarki nan da watanni masu zuwa.

Ta bayyana cewa ana tsara karin ta yadda zai zo da tallafi ga masu karamin karfi cikin masu amfani da wutar.

Mashawarciyar Shugaban Kasa kan Makamashi, Olu Verheijen, ce ta sanar da hakan a Babban Taron Shugabannin Lantarki na Kasashen Afirka da ke gudana a Dar es Salaam, hedikwatar kasar Tanzania.

A yayin taron ta gabatar wa mahalarta da shirin na Najeriya na kashe Dala biliyan 32 domin inganta wutar lantarki zuwa shekarar 2030.

Batun karin na zuwa ne bayan a bara gwamnatin ta yi ninka kudin wuta sau uku ga kwastomomi da ke amfani da Band A.

A yanzu kuma kamfanonin rarraba wutar lantarki, wadanda basuka suka riga suka yi musu katutu, sun matsa wa gwamnatin lamba ta bari su kara kudi domin samar da wutar yadda za su share hawayen kwastomominsu.

A watan Afrilun 2024 Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta yi karin kudin wuta da kashi 300%, daga N68 zuwa N225 a kan kowane kilowat ga masu amfani da Band A.

Da yake sanar karin, Mataimakin Shugaban NERC, Musliu Oseni, ya ce kashi 15% na masu amfani da wutar ne ya shafa, kuma zai inganta samuwar wutar.

Hakazalika Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa idan aka ci gaba da biyan tallafi ga masu amfani da Band A, yawan kudin da gwamnati ke biya na tallafin a shekara zai karu zuwa Naira tiriliyan biyu.

Amma dai daga bisani an rage kudin zuaw N209.5.

Sabon kafin farashi

Game da sabon karin kudin, hadimar shugaban kasan ta bayyana cewa Najeriya na kokarin samar da tsarin samun wutar lantarki gwargwadon yadda aka biya kudin, domin jawo masu zuwa jari a bangaren.

Ta shaida wa taron cewa, “Daya daga cikin kalubalen da muke  kokari magancewa nan da ’yan watanni masu zuwa shi ne komawa tsarin shan wutar lantarki gwargwadon yadda aika biya.

“Da haka ne bangaren zai tara kudaden da ake bukata domin jawo ’yan kasuwa masu zuwa jari tare da kare talakawa da masu rauni daga cuta.”

Alawar yara mai sanya maye ta shiga gari —NDLEA

NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje

Zazzabin Lassa ya kashe mutum biyu a Filato

Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki